BEFORE MARRIAGE
Yana kula da al amuranki
Yana kiranki a kodayaushe
Shi mai yawan nemanki ne
Kodayaushe cikin yi miki alkawarin baxantaba
iya rabuwa dake ba
Yayi alkawarin kasan cewa tare dake a kowanne irin yanayi
Shi mutum ne nagari
Yayi miki alkawarin aure
INDA MATSALAR TAKE
Ya nemi da ki bashi kanki
Kin tsorata da lafuzansa
Kin tsaya jinkiri kafin ki amince da bukatarsa
Amma daga baya sai kika amince domin kina gudun bacin ransa
Kinyi tunanin shi mutum ne nagari
Kinyi tunanin zai cika alkawarin da yayi miki
Ya ganki tsirara haihuwar uwarki
Yayi dukkan abinda yake bukatar yi dake
Kin bashi abu mafi daraja da kima da kike alfahari dashi
Shikuma yakasance cikin gagarumin farinciki
KIN BASHI KANKI KAFIN AURE
Sai yafara neman karin saduwa dake akai akai
Kin amince ya cigaba da kwanciya dake sau ba adadi
Sai kika fara ganin bakon sauyi daga gareshi
Ya fara nuna miki rashin kulawa kamar yadda yakeyi miki a baya
Yafara daukar zafi da yi miki fada akan dan kankanin laifi
Yafara jifanki da munanan kalmomi aduk lokacin da kuka samu sabani
Yafara ganinki a matsayin yar takura a gareshi
Yafara cin amanarki
KINSAN DALILIN FARUWAR HAKAN TO ZO KIJI
Saboda baki da wani abu na musamman da zaki bashi yaji kin birgeshi
Saboda baki da abinda zaiji yana dokinki
Saboda yana ganin kinyi arha sosai a gareshi
HABA YAR UWA ME KIKE TUNANI NE A BAYA ?
Kina tsammanin zai cigaba da yin tattalinki ne alhalin baki da wani abu da zaki birgeshi dashi ?
Kina tsammanin zai ga darajarki ne bayan kin zamo mace mafi arha a gurinsa ?
Kina tsammanin ya cigaba da kasan cewa tare dake bayan ya kwanta dake kuma babu abinda bai gani ba na daga private parts dinki ?
To dame kuma kike so ki kara birgeshi ?
Da me kuma zakiyi alfahari a matsayinki na ya mace a idanunsa ?
Zai kara gaba ne ya barki ya cigaba da bibiyar sauran mata
Zai cigaba ne da rayuwarsa kamar bai taba wata mu amala dake ba
Zai cigaba ne da rayuwarsa batare da damuwar sisin kobo ba a xuciyarsa
Baxai iya aurenki ba