Abin Da Sheikh Goni Aisami Ya Faɗa Min Yayin Da Na Ɗaga Bindiga Zan Harbe Shi, Sojan Da Ya Káshe Sheikh Aisami Ya Bayyana

Posted by

Abin Da Sheikh Goni Aisami Ya Faɗa Min Yayin Da Na Ɗaga Bindiga Zan Harbe Shi, Sojan Da Ya Káshe Sheikh Aisami Ya Bayyana

Sojan da ya káshe babban Malami a jihar Yobe Kofur John Gabriel, ya bayyana abinda Sheikh Goni Aisami ya faɗa masa yayin da ya ɗaga bindiga zai harbe shi.

Kofur John Gabriel ya ce;

“Yayinda muka kusa Jaji-Maji kuma tagogin motar na sauke, sai na faɗa masa ina jin ƙara ƙarƙashin motarsa, sai yace shima yana ganin akwai wani abu.”

“Sai ya faka motar. Yayin da ya tsaya a gefen hanya ya fita daga motar, sai na bi shi, bayan ya gama dubawa bai ga komai ba.”

“Ni kuma tuni na fito da bíndiga da harsashi lokacin da yake duba motar. Da bai ga komai ba, sai na nuna masa bíndiga, sai ya tambayeni, ‘Me na maka?” Ni kuma na bashi amsa, babu abinda kayi min.”

“Sai ya sake tambaya ta, ‘Kana son ka káshe ni ne?’ Sai na nace masa bana son káshe ka’ Sai yayi shiru. Sai na harba bíndiga don tsoratar da shi ina tunanin zai gudu. Amma bai gudu ba, sai ya shiga cikin motar, sai na bíndige shi.” Inji Kofur John

Source:Idon Mikiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *