Adam A zango Ali Nuhu da Laila sun koka kan Harin jirgin kasan kaduna

Posted by

Adam A zango Ali Nuhu da Laila sun koka kan Harin jirgin kasan kaduna

Jaruman sun kokan kan yadda harkar tsaro take basu tsaro a Nigeria inda suka ce gaskiya gwabnati saifa ta tashi tsaye ganin yadda kullum al’amarin ta azzara yake

Anjiyo Adam A Zango dai yana chacchakar gwabnati musamman ganin yadda mahaifiyar sa wato jihar Kaduna take fama da tabarbarewar rashin tsaro inda yace yanzu fa abin yakai Bama gida za a biyokaba har cikin jirgi ake bi ake kwamishe mutane

Sai dai shima ana bangaren Ali Nuhu ya magantu inda yace be kamata gwamnati ta zuba ido ana kashe jama’a ba babu gaira babu dalili yace ginshikin al’umma a rayuwa shine tsaro domin saida nutsuwa mutum kan iya komai

Ita dai jaruma Laila tace gaskiya lamarin yakan bata tsoro yanzu ace duk karfin gwabnati amma ace yan ta’adda sun gagareta shekara kusan goma ana fama da abu daya yaki karewa

 

 

Sai dai kuma jama’a kan cewa ai harda yan film din a wa’yanda suka bayar da gudummawa wajen kafa gwamnati me mulki yanzu kuma sai suzo suna kusheta kodan abun yazo kansu ne

Ta wasu bangaren kuma mutane kan yabawa jaruman wajen cire tsoro don fadawa gwamnati Gaskiya

Yayinda wasu kuma kance ai tunda basuyi magana ba sai da sukaga abin yaje kaduna duba da nanne hidkwatarsu idan aka cire Kano duk wani dan film kaji ance dan Kaduna ne to komadai da wacce manufa suka soki gwabnatin Allah ya kawo mana dauki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *