Anyi Artabu Tsakanin Jami’an Tsaro Da Ƴan Ta’adar Daji A Yankin Shinfiɗa Ta Ƙaramar Hukumar Jibia A Jihar Katsina…

Posted by

Anyi Artabu Tsakanin Jami’an Tsaro Da Ƴan Ta’adar Daji A Yankin Shinfiɗa Ta Ƙaramar Hukumar Jibia A Jihar Katsina..

Awasu Bayanai da suke fitowa daga ƙaramar hukumar Jibia ta jihar Katsina na nuni da cewa an ƙwana yin ba ta kashi tsakanin Jami’an tsaro da Ƴan Ta’adar daji da suka addabi wannan yankin ta ɓangaren Jamhuriyar Nijar.

Wani ma zaunin yankin na Shinfiɗa ta ƙaramar hukumar Jibia ya bayyana cewa tun cikin dare suke jin ƙarar rugugin harɓe harɓen Bindiga daga baya kuma sukaji wata ƙara mai ƙarfin gaske,

wanda daga baya suka gane cewa Motar Jami’an tsaro ce ta APC (Armoured Personal Carrier) ta taka wani abin fashewa inda Motar ta tarwatse. Kimanin Jami’an Sojoji biyu ne suka rasa rayukan su yayinda wasu kuma har yanzu ba’a gansu ba,

Jami’an tsaron dai sunyi ƙoƙarin korar maharan da aka ƙwatanta yawan su da sama da Dubu ɗaya ɗauke da muggan makamai.

Kazalika Suma mazauna wannan yankin Lamarin harin ya rutsa dasu Inda aka samu asarar rayukan da ba’a kaiga tantancewa ba kawo yanzu. Muna Adduar All

4 comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *