Ash-sheikh Dr Ahmad Abubakar Mahmud Gumi yayi zazzafan raddi bisa kama dan jarida dake jagorantar sasanci da kidnappers Tukur Mamu

Posted by

MALAM YAYI ZAZZAFAN RADDI

Ash-sheikh Dr Ahmad Abubakar Mahmud Gumi yayi zazzafan raddi wa Gwamnatin Shugaba Buhari bisa kama dan jarida dake jagorantar sasanci da kidnappers Tukur Mamu

Dr Ahmad Gumi yace a gaggauta sakin Tukur Mamu ya dawo su bashi hakuri domin kar ya janye akan aikin da yake yi domin neman zaman lafiya da ‘yan ta’adda, ko kuma wadanda suka kamashi su gaggauta kaishi Kotu idan sun taki gaskiya ba wai su cigaba da rikeshi ba

Malam yace wannan abinda ake yiwa ‘yan Arewa makirci ne, kuma jami’an tsaro da suka fito daga kudu su ke yakarmu ta karkashin kasa

Malam yace shima tsohon jami’in tsaro ne, yayi aikin tsaro, kuma ya san tsaro, saboda haka ya san sharrin hukumomin tsaro, har su Sardauna, Murtala, Maimalari, Ibrahim Badamasi Babangida da shi kanshi shugaba Buhari basu tsira da sharrin jami’an tsaro ba

Malam ya ja hankalin duk wani mai hankali sosai game da makircin da makiyanmu na cikin gida da suke tare damu a cikin hukumomin tsaro suke kullawa domin a hana yankin mu na Arewa zaman lafiya

Na daura bidiyo na Malam da yake wannan jawabi masu kama hankali a YouTube channel dina, Malamai jarumai masu fitowa su tona asirin makiyanmu muka rasa a yanzu, duk wanda bai fahimci halin da muke ciki ba ga link na bidiyo da Malam yake fayyace mana jawabai
👇

Allah Ka kare mana Sheikh Dr Ahmad Gumi (H)

kada kumanta kudinga muna share na post inmu zuwa ga abokaninku domin bamu qwarin guiwar kawomaku ingantattin sahihun labaran duniya a cikin harshen hausa dana turanci mungode da ziyartar shafin KuryaLoaded.ng dakunkayi

Idan kuna da tambaya ko wani labari da kuke son sanar da mu, ko tallata hajar ku kuna iya aika mana da sako a shafinmu na Facebook, ko tura sako a number admins dinmu +23408141702912

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *