Barawo Ya Sace Wayar Dan Sanda Bayan Yaje Belin Abokinshi Kamar yanda shafin amihad ya ruwaito
’Yan sanda sun ce lamarin ya faru ne lokacin da wanda ake zargin ya je caji ofis dinsu da ke Bolade, domin yin belin abokinsa da aka tsare.
Yar sanda mai gabatar da kara, Rachael Williams, ya ce wanda ake zargin ya shiga ofishin ne lokacin da wayar ke ajiye a kan tebur.
Kodayake ya musanta zargin satar wayar, amma ’yan sanda duk da haka sun gurfanar da shi kan zarge-zargen sata da shiga ofishin ba bisa ka’ida ba.
A cewar Rachael, gano satar wayar ya jefa ’yan sandan da ke bakin aiki cikin rudani, inda nan take Baturen ’Yan Sandan ofishin ya ba da umarnin gudanar da bincike.
Alkalin kotun, Mai Shari’a O.O. Akingbesote, ya bayar da wanda ake zargin beli a kan Naira 100,000 da kuma mutum biyu da za su tsaya masa.
Daga nan ne alkalin ya dage ci gaba da sauraron karar tare da ba da umarnin tsare wanda ake zargin a gidan gyaran hali na Kirikiri.
kada kumanta kudinga muna share na post inmu zuwa ga abokaninku domin bamu qwarin guiwar kawomaku ingantattin sahihun labaran duniya a cikin harshen hausa dana turanci mungode da ziyartar shafin KuryaLoaded.ng dakunkayi
Idan kuna da tambaya ko wani labari da kuke son sanar da mu, ko tallata hajar ku kuna iya aika mana da sako a shafinmu na Facebook, ko tura sako a number admins dinmu +23408141702912