KANNYWOOD

Da mutane ne suke bada makullin Aljanna da baza su baiwa ‘Yam Fim ba, cewar jaruma Hauwa Waraka

A wata tattaunawa da BBC Hausa suka yi da jarumar masana’antar kannywood “Hauwa Waraka”, a cikin shirin su na Daga Bakin mai ita a ranar Alhamis ta bayyana takaicaccen tarihin rayuwarta.

Da farko ta fara da bayyana cewa, sunanta Hauwa Abubakar amma an fi saninta da Hauwa Waraka, an haifeta a garin Jos amma a garin Kano ta girma.

Da aka tambayeta yadda aka yi ta shiga harkar fim sai tace, da farko bata san menene fim ba ma akwai wasu ‘yan uwanta ne da suka kai ta Sabon Titi dake Kano inda asalin ‘yan fim suke, daga nan ta dan fara shiga harkar jifa-jifa.

An tambayeta fim din da ta fara inda tace, ta fara da kananu ne wadanda ba ita bace jarumar da ta haska fim din, don ko shirin Waraka wanda tayi fice dashi ba ita bace babbar jaruma a fim din.

DUBA: Wannan Bidiyon Rawar Fatima Ali Nuhu Yabarmata Baya Da Qura

Ta kara da cewa, bayan ta dan yi fina-finai ta bar industiri na kusan shekaru 5 zuwa 7 wanda daga bisani ta dawo, dama kuma tun asali bata san menene fim ba dama kawai tana yi ne sama-sama.

Da aka tambayeta dalilin da yasa take fitowa a mutimiyar banza sai tace, ta san babu kyau a musulunce ayi shaye-shaye da sauransu, amma kawai suna yi ne don fadakarwa kuma ita har yau bata shaye-shaye.

Ta ce, bata jin dadin kallon da mutane suke yi mata, amma kuma tunda babu mai wuta ko Aljanna ko kadan bata damuwa.

Ga cikekkiyar bidiyon shirar tasu a kasa domin ku kalla.

Na yarda da Allah, na yarda da mazonnin Allah, na yarda da sunnoninsa, na yarda da mala’ikunsa, na yarda da littafansa, kuma na yarda da ranar kiyama, kuma na yarda da kalmar La’ilaha illallahu Muhammadar rasulullahi sallallahu alaihi wa sallam.

Kuma ni abinda nake gaya wa al’umma na san mutum dai bai da makullin wuta bai da makullin Aljanna. Balle yace ai nine mai makkulin wuta, wuta zan kai ka ko kuma nine mai makullin Aljanna, Aljanna zan kai ka.

Don majority mutane kallon da su ke mana, inda su suke bada Aljanna, majority mutane ba za su ba dan fim ba. Magana ta gaskiya, saboda akwai mutanen da ko sunana aka kira, sai kaji sun ce wannan makamashin wutar? Ni kuma naga baka da wuta baka da Aljanna. Allah shi ke bada ita ba mutum ba.

READ ALSO:  EP. 103 OF IZZAR SO SABON SALO

Mr Kurya

The Name is Kurya An Full Time Blogger | Entrepreneur | Online Promoter| Web Designer | Web/App Developer | Content Writer | Your Number 1 B*D A** Blogger 😏 Follow Us Social Media Below

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Sorry You need to turn off your adblocker to browse on this blog please