Kamfanonin biredi a Najeriya sun yi barazanar tafiya yajin aiki sakamakon ƙarin farashin kayayyakin haɗi.
- Advertisement -
Jaridar Punch a Najeriya ta ruwaito ƙungiyar ‘Association of Master Bakers and Caterer of Nigeria’ wadda ta ce farashin fulawa da sikari da sauran kayan haɗi da ake amfani da su wurin yin biredi duk sun yi tashin gwauron zabi.
Ƙungiyar ta kuma ƙalubalancin gwamnatin Najeriya kan zargin nuna halin ko in kula dangane da wannan batu inda ƙungiyar ta yi barazanar tafiya yajin aiki daga ranar 13 ga watan Yulin 2022.
Ko a kwanakin baya dai sai da aka ƙara kuɗin biredi a Najeriya sakamakon ƙarin farashin kayayyaki.
- Advertisement -
One Comment