Ina da shekara 28, iyayena sun rasu tun ina da shekara 14. Na daina makaranta saboda babu wanda zai rinƙa biya min Ƙuɗin makaranta.

Posted by

Ina da shekara 28, iyayena sun rasu tun ina da shekara 14. Na daina makaranta saboda babu wanda zai rinƙa biya min Ƙuɗin makaranta.

Daga inbox dina…. Ina da shekara 28, iyayena sun rasu tun ina da shekara 14. Na daina makaranta saboda babu wanda zai rinƙa biya min Ƙuɗin makaranta.

Na hadu da wani saurayi lokacin ina 17yrs kuma ya mayar da ni makaranta. Amma shi yana Sana’ar sayar da ‘ya’yan itatuwa ne a kan titi amma a hakan yake biya min kudin makaranta.

Daga baya wannan saurayin nawa ya samu aiki a matsayin direban babbar mota ya tura ni jami’a.Yanzu ina aiki a matsayin lauya.

Saidai Matsala na shine naji bazan iya cigaba da wannan alaka ba domin wannan saurayin ba irin namijin da zan aura bane! !!!!

Ku bani shawara ta yaya zan iya gaya masa cewa shi ba irina bane ba tare da ya cutar da shi ba?

Ina godiya da ya tura ni makaranta amma ba zan iya zama da shi ba kuma! Ina son wani a cikin ajina ba direban babbar mota ba! !! Don Allah a bani shawara…Ba zagi🙏

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *