LABARAI

Innalillahi Wainna Ilaihi Raji’un: Kukalli Wannan Daliban da ta rasa Kafarta Awanni Kadan Da Kammala Rubuta Jarabawarta Ta Secondary

Innalillahi Wainna Ilaihi Raji’un: Kukalli Wannan Daliban da ta rasa Kafarta Awanni Kadan Da Kammala Rubuta Jarabawarta Ta Secondary

Wata daliba ‘yar shekara 16 da ta yi rashin sa’a domin ta rasa kafarta bayan ta rubuta jarabawar karshe a Sokoto.

Fatima A gadon Asibiti Bayan Yanke Mata Kafa

Wata Daliba mai suna Fatima ta rasa Kafarta awa guda bayan ta fito rubuta jarabawarta ta karshe a wata Makaranta a Jihar Sokoton Tarayyan Najeriya.

Fatima ta ci karo da wani mummunan hadari ne a daidai lokacin da suke murna da farin cikin rubuta jarrabawarta ta karshe, abokanan karatunta maza kuma suna wasa da mota yayin da Fatima da kawayenta suke gefe suna kallo.

Kwatsam ba a ankara ba sai mota guda tayi kan Fatima inda nan take ta banke ta ta kuma karairaya mata kafa guda.

Hoto: Kafin Fatima ta samu (hagu) da kuma bayan ta samu hatsari (dama).

Cikin murna Fatima ta samu waya daga mahaifiyarta cewa zata zo ta dauke ta idan sun kammala rubuta jarabawar.

READ ALSO:  Daga Karshe An Shiga Kotu Kan Shari’ar Fatima Wacce Aka Yankewa Kafa

Fatima da kawayenta suna wajen makaranta suna jiran zuwan mahaifiyarta. Sai Allah ya kawo wannan kaddara akan Fatima yayin da kawayenta guda biyu suka tsallake rijiya da baya.

A kasa hoton Fatima ne bayan an yanke mata kafar.

Daga nan ne aka kai Fatima cibiyar Trauma da ke asibitin koyarwa na Jami’ar Usman Danfodiyo (UDUTH) da ke Sakkwato, inda likitoci suka bayyana cewa barnar da aka yi mata ya wuce ceto, inda suka ce dole ne a yanke kafarta domin ceto rayuwarta.

Kamar yadda Aminiya ta ruwaito, Fatima ‘yar shekara 16 daliba ce a makarantar Khalifa International Model School, makarantar da ke kan titin Nana Asmau a Sakkwato.

Fatima ta bayyana cewa ta rubuta jarabawar JAMB ta bana kuma ta samu maki 230.

Ta ce burinta shi ne ta zama likita, ta ce abin da ya faru da ita ba zai hana ta cimma burinta ba.

Mr Kurya

The Name is Kurya An Full Time Blogger | Entrepreneur | Online Promoter| Web Designer | Web/App Developer | Content Writer | Your Number 1 B*D A** Blogger 😏 Follow Us Social Media Below

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Sorry You need to turn off your adblocker to browse on this blog please