Jarumin Finafinan Hausa Ya Jibgi Wata Malamar Islamiya Sabida Ta Daki ‘Yar Sa

Posted by

Jarumin wasan Hausa, Ari Baba, ya jibgi malamar Islamiyya saboda hukunta ‘yarsa

Ana zargin fitaccen jarumin wasan barkwanci a masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood, Aminu Ari Baba, da jibgar wata malamar Islamiyya dake yankin Kofar Nasarawa a jihar Kano, bisa hukunta ‘yarsa mai suna Hafsa da malamar tayi a makaranta, sakamakon laifi da suka aikata.

Malama Safiya Nasir, wacce ake zargin Ari Baba ya jibga, tace tana zaune a cikin Aji ta biya musu karatu, sai yarinyar ta ke cin Cingam tare da wata Dalibar a kusa da ita, bayan kuma dama wani malami mai suna Malam Sulaiman yayi musu magana, saboda haka ta dauki Bulala da daki ta kusa da ita, amma ita Hafsa sai ta ce ba za’a dake ta ba, har sukayi sa’insa, ana fara yi mata Bulala sai ta zube a ƙasa wanwar da nufin ta tayar da Aljanu.

“Ina cikin tafiya ne sai ga mahaifinta ya zo, yana cewa, ke Hafsa waye ya doke ki, wacce malamar ce ta dake ki? Ana fada masa kawai sai ya janyo ni ya kifa min mari, ya fara taka bayana da Takalminsa.”

A nasa bangaren, Ari Baba, yace ya yarda yayi kuskure, kuma ya amsa laifinsa, amma yayi rantsuwa da mahalicci akan cewa, gefen Dankalinta kawai ya doka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *