KANNYWOOD

Lamarin Tahir Fagge Akwai Wadanda Sunkamashi Asiri acikin lamarinsa

 

Lamarin Tahir Fagge  Akwai Wadanda Sunkamashi Asiri acikin lamarinsa

Abinda Tahir Fagge Yake Yi Ba Yinsa Ba Ne Asiri Akai Ma Sa

Daga Gen Sunusi

Tahir Fagge Addu’a yake buƙata ba zagi da tsinuwa ba daga gareku, domin shi wannan FLOOR ɗin da kuke gani yana hawa yayi rawa ba ordinary FLOOR ba ne da muke gani wani waje ne mai masifar kiranye ba kowane yake hawansa ya daina cikin sauki ba.

Duk wanda bai taɓa taka ƙafarsa a Gidan Wasa ba shine bai san masifar kiranyen gidan ba, idan zuwa gida wasa ya kamaka barinsa aiki ne ɓare kuma ace kana hawa FLOOR kayi rawa.

A Gidan Wasa ne zaka ga duk masifar son da Namiji yake yiwa Motarsa amma yazo ya bayar da ita ya koma gida a ƙasa wani har bashi yake ci don yaje yayi liƙi ya dawo kasuwa a ɗaureshi.

Nasan mutanen da suke siyarda ƙadarorinsu don suje gidan wasa su liƙa kuɗi. Ko last week akwai wanda aka bani labari saboda karayar arziki ya saka gidansa a kasuwa zai siyar ƙarshe sai abokinsa ya bashi kuɗi ƙarshe ance an ganshi a gidan wasa yana liƙa kuɗin.

Akwai wani babban mutum saboda tsabar zuwa Gidan Wasa sai da ya auro Chairlady (Shugabar Mata Ta Gidan Wasan) Duk da Mutumin a shekaru yayi jika da ita sannan a mu’amala ta zahiri mutumin kirki ne amma sai ga shi an jarrabeshi da zuwa gidan wasa jikokinsa suna rawa yana yi musu liƙi.

Gidan Wasa wata Duniya ce mai zaman kanta wacce shigarta babu ranar fita sai idan Allah ya taimakeka! Koda kuwa babu wanda ya yi maka asiri bare kuma Tahir Fagge da ake cewa asiri aka yi masa.

Duk da abinda yake yi ba daidai ba ne ba amma fa saboda shi Ɗan Film ne aka fi yayata abin saboda sananne ne amma idan kaje Gidan Wasa zaka ga wanda ya kusa haifarsa yana rawa a FLOOR da jikokinsa, Allah Ya a shirye mu, Amin.

©Zuma Times Hausa

READ ALSO:  Wanan Bidiyon Nuna Tsaraicin Da Maryam Babban Yaro Ta Fitar Ya Fusata Masoyanta

Mr Kurya

The Name is Kurya An Full Time Blogger | Entrepreneur | Online Promoter| Web Designer | Web/App Developer | Content Writer | Your Number 1 B*D A** Blogger 😏 Follow Us Social Media Below

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Sorry You need to turn off your adblocker to browse on this blog please