Nafi Sha’awar Ƙananan Yara Fiye Da Manyan Mata – Inji Tsohon Da Aka Kama Ya Yiwa Ƙaramar Yarinya Fyaɗe

Posted by

An kama wani mutum mai shekaru 57, mai suna Chidi Obieze a ranar Laraba bisa zarginsa da lalata wata yarinya ƴar shekara 10.

Mutumin wanda ya ce shi dan asalin Egbem Ozubulu ne a karamar hukumar Ekwusigo ta jihar Anambra, an kama shi ne a unguwar Oraifite da ke makwabtaka da ita, saboda yadda ya saba da lalata ƙananan yara.

Daga iƙirarin da ya yi a wani faifan bidiyo da aka nada, ya ce ya shafe shekaru 10 yana lalata ƙananan yara mata.

Mutumin da matasan Oraifite suka kama shi suka daure shi, ya roki a yi masa sassauci, inda ya ce a shirye ya ke ya daina idan har aka sake shi a halin yanzu.

A cikin wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, Obiaze ya ce: “Ni ma ina son mata da suka manyanta, amma na fi son Ƙananan yara.

“Na yi wannan kusan shekaru 10 yanzu.”

Da aka tambaye shi ko me yake yi da yaran, sai ya ce, “ina taɓa ta ne kawai a lokacin da aka kama Ni. Kawai taɓa nake yi a farjin ta, aka kama Ni.

DAILY POST, duk da haka, ta kasa tantance abin da ya faru da mutumin daga bayan wannan bidiyon.

Kokarin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Toochukwu Ikenga inda aka miƙa mutumin ga ‘yan sanda a yankin bai haifar da da mai ido ba domin har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a kai ga samun nasarar samun layin wayar sa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *