Sadio Mane shine na 10, cikin yan wasan Afirka da zai buga tamaula a Bayern Munich
Sadio Mane shi ne na 10 daga Afirka da zai buga wa Bayern Munich tamauala, bayan da ta fara daukar Noussair Mazraoui daga Ajax da zai koma kungiyar a bana.
Mazraoui, mai tsaron bayan tawagar Morocco zai koma Munich ranar 1 ga watan Yuli, saboda haka shi ne na tara daga Afirka a kungiyar da ta lashe Bundesliga a kakar da ta wuce.
Mane dan wasan tawagar Senegal, wanda ya koma Munich daga Liverpool a bana, shi ne na biyu da zai taka leda a Bayern daga Senegal, bayan Bouna Sarr.
Sauran ‘yan wasa bakwai daga Afirka da suka buga wa Bayern Munich tamaula sun hada da Samuel Kuffour da Kwasi Wriedt dukkansu daga Ghana.
Sauran sun hada da Eric Maxim Choupo-Moting da Franck Evina da Louis Ngwat-Mahop dukkansu daga Kamaru da Medhi Benatia daga Morocco da kuma Pablo Thiam daga Guinea.
Mane wanda ya ci kwallo fiye da 100 a Liverpool da daukar Champions League da Premier League da FA Cup da League, ya kuma lashe kofin Afirka a Fabrairu a Kamaru.