Tabbas akwai ƙanshin gaskiya a maganar Safara’u, da ta ce kaso saba’in na mata suna ɗaukan tsiraicinsu koda kuwa ba wani zasu turawa ba.
Wani abu da na daɗe da fahimta akan waya mai camera shine, tanada wani tasiri sosai wajen rinjayar hankalin mace tayi ta shirme a gaban camera. Kuyi tunani yanda mace
take idan ta samu madubi to bare kyamarorin yanzu da har taimakawa mutum suke wajen tatso kyanshi. Akwai hotunan tsiraicin da ka gani kasan ba da manufar turawa wani aka yi ba,
mata suna son ɗaukar kansu hoto a kowanne yanayi suke ciki, kuma da yawa suna goge abinda suka ɗauka ne a nan take, saidai abinda basu sani ba shine,
ana yin katari wayar ta adana wannan hotunan ko videos ɗin a wani waje wanda har wata rana ka bai wa wani wayar wajen binciken shi ya gano su. (Masana ciki da bai na waya sun san me nake nufi.)
Dan haka maganar Safara’u bata yiwa mata adalci ba bata taso ba.