LABARAI

Tinubu Ya Tafi Kasar Faransa Wajen Wani Taro Mai Muhimmanci

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya fice daga kasar a safiyar yau Litinin zuwa kasar Faransa bayan ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Tunde Rahman na ofishin yada labarai na Tinubu ya fitar ranar Litinin, ya ce shugaban nasa ya tafi birnin Paris na kasar Faransa domin gudanar da wasu muhimman taruka.

Ya lura cewa ana sa ran dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC zai dawo kasar nan ba da jimawa ba ba tare da bayyana takamaiman ranar ba.

Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito tun da farko kafin tafiyar tasa, Tinubu ya halarci taron baje kolin wani littafi mai suna, ‘Mr. Speaker’ and launch of legislative mentoring initiative in commemoration of the 60th birthday of the Speaker of House Representatives, Femi Gbajabiamila, a Abuja ranar Lahadi.

A Wani Labarin Kuma Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwanso, ya ce jam’iyyar APC da PDP sun gaza a tsawon shekaru wajen samar da tallafi ga tattalin arzikin jama’a da cigaba ga ‘yan Najeriya a dukkan bangarorin mulki.

Tsohon gwamnan jihar Kano wanda ya bayyana hakan a karshen mako a Ado-Ekiti, babban birnin jihar Ekiti yayin wata ziyarar tuntuba da ya kai jihar ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi watsi da jam’iyyun biyu a babban zaben shekara mai zuwa, yana mai cewa dukkan alamu na ci gaban zamantakewa da tattalin arziki kullum suna tashi a cikin mummunan gefe.

Ya kuma nuna rashin jin dadinsa kan yadda hanyar Akure zuwa Ado ke tabarbarewa, inda ya yi Allah-wadai da yadda gwamnatin tarayya da gwamnatocin Jihohi karkashin jam’iyyar APC suka yi watsi da jama’a suna shan wahala a kan hanya.

Kwankwaso ya bukaci jama’a da su ci gaba da rike amana tare da NNPP domin kawo sauyi ga kasar nan da dora ta kan turbar ci gaba.

Ya bayyana cewa jam’iyyar na fuskantar karuwar mambobi a cikin ‘yan watannin da suka gabata tun bayan da ya shiga dandalin.

Kwankwanso ya bayyana cewa matsalar rashin tsaro da ake ta fama da ita a fadin kasar nan da kuma munanan manufofin tattalin arziki wadanda suka haifar da fatara, rashin aikin yi, hauhawar farashin kayayyaki sun isa ya sa jama’a su yi watsi da jam’iyya mai mulki, ya kara da cewa, “Hanyar da muke tafiya a yanzu ita ce hanya guda ta bala’i. a kasar.”

READ ALSO:  Tohfa Naziru sarkin waka _ ya saki zazzafar wakar cin mutunci ga Bula tunubu

Mr Kurya

The Name is Kurya An Full Time Blogger | Entrepreneur | Online Promoter| Web Designer | Web/App Developer | Content Writer | Your Number 1 B*D A** Blogger 😏 Follow Us Social Media Below

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Sorry You need to turn off your adblocker to browse on this blog please