DUNIYARMU AYAU

Tirkashi Yau Wani Dan Daidaita Sahu Yabani Mamaki A Kano

Tirkashi Yau Wani Dan Daidaita Sahu Yabani Mamaki A Kano

TABBAS DUK LALACEWAR ZAMANI BAKA RASA NA KIRKI

Yau wani Ɗan Adai-daita sahu a kano ya ban mamaki.

Ya ɗaukeni daga cikin gari zai kaini gurin da zamu yi POP wato Federal Secretary wajen Katsina Road, Ina Sauka bayan mun rabu da kamar 5m sai na duba wayata babbar ban gantaba, aiko sai na kira, tana shiga sai ya ɗauka yace a kekensa na barta amma zai dawomin da ita, na dai amsa da to Nagode.

Abinda ya ban tsoro yaron sam babu siffar nutsuwa ko tsoron Allah a tare da shi don haka gaba ɗaya na karaya.

Bisa mamaki kawai sai ga shi mun haɗu a Bacirawa wajen Masallacin Mariya ya kawomin wayata, ya kuma cemin nan unguwar su.

Tabbas duk lalacewar zamani to na Allah basa ƙarewa, sannan shi tsoron Allah ba’a riga ko siffa yake ba.

Allah ya ƙara sadamu da mutanan kirki, shi kuma wanann yaro muna Addu’ar Allah ya azurtashi da arziki na halali.

READ ALSO:  Ina Da Karfin Jiki, Lafiyayye Ne Ni, Tinubu Ya Warware Jita-jitar Rashin Lafiya A Bidiyo

Mr Kurya

The Name is Kurya An Full Time Blogger | Entrepreneur | Online Promoter| Web Designer | Web/App Developer | Content Writer | Your Number 1 B*D A** Blogger 😏 Follow Us Social Media Below

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Sorry You need to turn off your adblocker to browse on this blog please