LABARAI

Wani Lauya zai kai Karar Hukumar Hisbah kotu a kan waƙar Gwanja mai taken Chass “Asosa”

Lauya zai kai Hisbah kotu a kan waƙar Gwanja mai taken “Asosa”

Wani lauya a jihar Kano, Barista Badamasi Sulaiman Gandu, ya yi barazanar maka Hukumar Hisbah ta jihar Kano a gaban kotu, matukar ta gaza dakatar da shahararren mawakin nan, Ado Isa Gwanja, daga fitar da wata sabuwar waka da ya yi mai taken “Asosa”.

A makon nan ne dai Gwanja ya saki somin-taɓin waƙar a kafafen sada zumunta, inda a ka gano shi yana bin wakar tare da sosa jikinsa cewa kaikayi ya kama shi.

Da ya ke zantawa da manema labarai a yau Laraba, Barista Gandu ya ce tuni ya aike da takardun gargaɗi na kwanaki uku ga hukumomin Hisbah da Hukumar Shari’a ta jihar Kano domin su gaggauta dakatar da mawakin daga fitar da sabuwar wakar.

Barr. Gandu, wanda ya zargi mawakin da yin amfani da kalaman da basu daceba acikin waƙoƙinsa, ya nuna cewa barin irin waɗannan wakokin a cikin al’umma zai kawo cikas wajen tarbiyyar yara masu tasowa.

Lauyan ya ce, kamata ya yi gwamnatin jihar Kano ta ɗauki mawakin aiki a karkashin hukumar Hisbah domin yin amfani da hikimarsa wajen faɗakar da al’umma saɓanin yadda ya ke amfani da hikimar ta wata hanya daban.

A ƙarshe, lauyan ya jaddada barazanar maka hukumar Hisbah agaban kotu matukar ta haura kwana uku bata dakatar da mawakin daga fitar da sabuwar waƙar ba.

READ ALSO:  Yan Bindiga Sun Kashe Sojojin Dake Tsaron Buhari A Abuja

Mr Kurya

The Name is Kurya An Full Time Blogger | Entrepreneur | Online Promoter| Web Designer | Web/App Developer | Content Writer | Your Number 1 B*D A** Blogger 😏 Follow Us Social Media Below

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Sorry You need to turn off your adblocker to browse on this blog please