LABARAI

Wata Karuwa Ta Yanke Farjin Abokiyar Aikinta da Reza Saboda Kwastoma

Rundunar yan sandan kasar Ghana sun kama wata ‘yar Najeriya da ke karuwanci a yankin Ashanti kan zargin amfani da reza wajen yanke farjin abokiyar sana’arta.

Mai laifin wacce aka bayyana a matsayin magajiya uwar dukkan karuwai a Dichemso Plaza ta kuma yi amfani da rezan wajen yayyaga fuska da cinyoyin matar kan zargin ta kwace mata daduronta, shafin LIB ya rahoto.

An tattaro cewa wacce ake zargin mai suna Bella, ta gargadi takwarar tata mai suna Ruth da ta rabu da wannan mutumin saboda shine babban kwastomanta.

Hakazalika an ce ta yi barazanar sauyawa Ruth kamanni idan har ta ki jin gargadinta na rabuwa da daduron nata.

Sai dai kuma, ita wanda abun ya ritsa da ita ta ki jin gargadin, hakan yasa Bella da wasu mutum hudu suka tare ta a hanya sannan suka tikata da kasa.

Daga bisani sai suka rirrike hannaye da kafafunta inda suka ba Bella damar yayyaga mata fuska da farjinta.

Har yanzu ba a kama sauran mutum hudu da suka aiwatar da muguntar tare ba domin sun tsere bayan da suka samu labarin kamun Bella.

READ ALSO:  Allahu Akbar Kukalli bidiyon Hira Da Yaro Me Basira Wanda Ya Gina Gadar Sama

Mr Kurya

The Name is Kurya An Full Time Blogger | Entrepreneur | Online Promoter| Web Designer | Web/App Developer | Content Writer | Your Number 1 B*D A** Blogger 😏 Follow Us Social Media Below

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Sorry You need to turn off your adblocker to browse on this blog please