KANNYWOOD

Yadda Hidimar bikin Lilin Baba da ummi Rahab ya kasance

Yadda Hidimar bikin Lilin Baba da ummi Rahab ya kasance


Kamar yadda Tashar Tsakar Gida ta nuna, manya-manya jarumai sun samu damar halartar daurin auren Lilin Baba da Ummi Rahab, amma banda Adam A. Zango.

- Advertisement -

Ali Nuhu shi ne wakilin ango inda ya amsar masa auren amaryarsa kuma bidiyon wurin daurin auren ya tabbatar da hakan.

Manyan jarumai maza sun yi nasarar zuwa wurin daurin auren inda su ka yi wa jaruman kara tun daga Ali Nuhu, Umar M Sherif, TY Shaban da sauransu.

- Advertisement -

Bayan kammala daurin auren an zarce wurin cin abinci wanda bisa bidiyon da ya bayyana, an bankare rago kowa na ta yanka yana sa albarka.

Mutane da dama sun yi mamakin rashin zuwan Adam A Zango kasancewarsa tsohon ubangidanta, sai dai ana tunanin ya yi hakan ne don zaman lafiya.

Ya yi gudun zuwa wurin wata tarzoma ta tashi daga wurin yaransa ko kuma habaici ko makamancin hakan, don haka kada ayi badi ba rai.

- Advertisement -

Idan ba a manta ba, a shekarar da ta gabata rikici ya hautsine bayan ya cire jarumar daga shirinsa mai dogon zango, Farin Wata.

Hakan ya janyo rikici iri-iri har yake gwada cewa yana kokarin yi mata tarbiyya amma yayanta ba ya goyon bayan haka. Shiyasa ya cireta idan ta lalace kada ya zama a karkashinsa ne hakan ta auku.

A bangaren yayanta Yasir Ahmed, ya tabbatar da cewa Adam Zango ya nemi aurenta ne amma daga baya bai dake waiwayarsu ba. Hakan ya bata damar kula samari.
A cewarsa, iya gwargwado ya san yarinyar tana da tarbiyya daidai gwargwado kuma da zarar ta samu mijin aure za ta yi aurenta.

- Advertisement -

A bangarenta ta bayyana cewa ta dauki Adam Zango a matsayin Ubanta ne, hakan ya sa ba za ta iya aurensa ba.
Sai kuma farkon shekarar nan batun Lilin Baba ya kunno kai da duminsa. Wanda babu jimawa sai aure ya kammala.

Lilin Baba yana cikin mawaka kuma jarumai masu tasowa masu rufin asiri, don Allah ya azurta shi tun daga motocin hawa, gidaje da sauransu.

READ ALSO:  Cikin Fushi Ali Nuhu Ya Yi Martani Ga Buhari Akan Bidiyon Zane fasinjojin Jirgin Kasa

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Sorry You need to turn off your adblocker to browse on this blog please