LABARAI

Yadda Hotunan Wani Magidanci Bahaushe Tareda Iyalansa Ya Janyo Cece-Kuce a Kafar Sada Zumunta

Yadda Hotunan Wani Magidanci Bahaushe Tareda Iyalansa Ya Janyo Cece-Kuce a Kafar Sada Zumunta

Wani ‘dan Najeriya yayi shagalin bikin sallah babba inda har ya bayyana hotunansa tare da matansa uku reras da ‘ya’yansa 19.

Bawan Allah mai suna Baba Lawal, ya wallafa kyawawan hotunan ne a ranar Lahadi, 10 ga watan Yulin 2022 a shafinsa na Facebook.

A hotunan sun yi ankon kaya kalar kasa mai duhu yayin da matan suka saka hijabai kalar kayan mijinsu da ‘ya’yansu sannan suka sanya niqabai a fuskokinsu.

Lawal, wanda ‘dan asalin jihar Kwara ne, yana koyarwa a kwalejin ilimi ta Umar Bn Khattab dake Kaduna kuma shine sakataren hukumar Hisbah na jihar Kaduna kamar yadda bayanansa na shafinsa a Facebook suka nuna.

Gadai jerin hotunan nasu akasa tareda Iyalansa


READ ALSO:  Masha Allah Yanzu Yanzunan: An Zabi Farfesa Sheikh Ibrahim Ahmad Makari A Matsayin Limamin Ka’aba

Mr Kurya

The Name is Kurya An Full Time Blogger | Entrepreneur | Online Promoter| Web Designer | Web/App Developer | Content Writer | Your Number 1 B*D A** Blogger 😏 Follow Us Social Media Below

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Sorry You need to turn off your adblocker to browse on this blog please