LABARAI

Yadda jami’an tsoron Nigeria suka kama wani kasurgumin me sayarwa yan Bindiga makamai

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana irin namijin aikin da jami’an soji suka yi a cikin kwanakin nan Daga ayyukan, rundunar ta bayyana cewa an kama wasu jiga-jigan ‘yan ta’addan da suyka addabi sassan kasar nan Rundunar ta kuma yabawa jami’ai, inda ta nemi su ci gaba da gashi tare da ragargazar tsagerun ‘yan ta’adda

Kafar labarai ta Channels ta ruwaito cewa, rundunar sojin Najeriya ta ce ta kashe ‘yan ta’adda shida a fagagen ayyukan ta daban-daban. Mahukuntan sojojin sun kuma ce sojojin sun kama wasu da ke hada kai da maharan, ciki har da wani fitaccen dillalin bindigu da kuma samar da kayan aikin Boko Haram. Wanna na fitowa ne daga wata sanarwa da kakakinta, Manjo Janar Bernard Onyeuko ya fitar, hedkwatar tsaro.

Sanarwar ta bayyana cewa, dakarun Operation Hadarin Daji sun amsa kiraye-kirayen mazauna kan barnar da ‘yan ta’adda suka yi a Rafin Dankura da ke karamar hukumar Bakura a jihar Zamfara inda suka yi awon gaba da wasu fararen hula.

Janar Onyeuko ya ce sojoji sun yi artabu da ‘yan ta’addan kuma a cikin haka ne sojojin suka ceto shida daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su tare da kashe biyu daga cikin ‘yan ta’addan.

Onyeuko ya bayyana cewa: “Abubuwan da aka kwato sun hada da AK 47, gurneti mai girman 1×36, wayoyin salula 2 da kudi 211,915.00

An dakile ‘yan ta’adda tare da kame wasu Hakazalika a ranar 21 ga watan Yunin 2022 a martanin da sojojin suka yi a kan ayyukan ta’addanci, sun yi tuntubar ‘yan ta’addar da suka yi garkuwa da wasu a Maigora da ke karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina tare da kashe ‘yan ta’adda biyu a cikin aikin.

Janar Onyeuko ya ci gaba da bayyana cewa dakarun Operation Whirl Stroke sun kama wani kasurgumin dillalin bindiga mai suna Ardo Manu Andulrahaman Maranewo a ranar 20 ga watan Yunin 2022, rahoton Vanguard

Maranewo wanda ya kasance cikin jerin sunayen wadanda jami’an tsaro ke nema ruwa a jallo an ce ya kware wajen sayar da makamai ga ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane a jihar Taraba.

Hakazalika, a ranar 20 ga watan Yuni, sojojin bataliya ta 151 na Operation Hadin Kai tare da hadin gwiwar CJTF da ke sintiri na tabbatar da tsaro sun ragargaji ‘yan ta’adda a kan hanyar Bama-Pulka. An kashe biyu daga cikin ‘yan ta’addan, sannan an kwato bindigogi da harsasai na gida guda biyu daga hannunsu.

A wannan rana ne wani dan ta’addan Boko Haram, Malam Modu Rija ya mika wuya ga sojojin Najeriya a yankin Tashangoto. Kayayyakin da aka kwato daga hannunsa sun hada da bindiga kirar AK 47 guda daya, da gurneti mai girman 1×36, da harsashi 26 na alburusai masu girman 7.62mm. Hakazalika, a ranar 21 ga watan Yunin 2022 sojoji sun kama wani dan Boko Haram, Malam Abacha Usman a Benishek da kuma wani mai safarar kayan aikin ta’addanci, Mallam Ibrahim Gira.

An kama su ne a hanyar Dambua zuwa Biu duk a jihar Borno. Janar Onyeuko ya ce, rundunar sojin ta yaba da kokarin da sojojin ke yi, ya kuma kara da cewa suna kara karfafa gwiwar su da su ci gaba da gudanar da ayyukansu na hedkwata na tare dasu.

‘Yan bindiga sun yi awon gaba da basaraken gargajiya a wata jiha A wani labarin, wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da basaraken al’ummar Isuokoma mai cin gashin kansa a karamar hukumar Onicha ta jihar Ebonyi, Eze Ambrose Ogbu.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, wasu da har yanzu ba a tantance ko su waye ba sun yi awon gaba da sarkin ne a daren ranar Laraba a fadarsa da ke Isu a yankin karamar hukumar.

Wata majiya mai tushe da ta nemi a sakaya sunanta ta tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin jaridar a Abakaliki a ranar Alhamis.

READ ALSO:  8 saboda rashin biyan hain Miji kotu ta raba auren da ya Shekara

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Sorry You need to turn off your adblocker to browse on this blog please