Yanzu Yanzu Wato Kotu a Jihar Kano Tayanke Hukuncin Kisa Ga Wanda Yakashe Haneefa

Posted by

Yanzu Yanzu Wato Kotu a Jihar Kano Tayanke Hukuncin Kisa Ga Wanda Yakashe Haneefa

Wata babbar kotu a jihar Kano dake Arewacin Najeriya ta yanke hukuncin kisa kan Abdulmalik Tanko, kan samun sa da laifin kashe dalibarsa mai suna Hanifa Abubakar, kamar yadda BBC Hauwa suka kawo rahoton.

Mai Shari’a Usman Na’abba dake jagorantar karar ne ya yanke hukuncin a ranar Alhamis 28 ga watan Yulin 2022.

Ana zargin malaminta Abdulmalik Tanko ne ya sace ta a watan Disambar 2021 tare da kashe yarinyar mai shekara biyar, kana ya binne gawarta a gidansa.

Kisan nata ya ja hankalin duniya inda dubban mutane, har da shugaban Najeriya
Muhammadu Buhari suka yi tur da shi.

Bayanai sun tabbatar da cewa, wasu mutane ne suka dauke ta a babur mai kafa uku da ake kira A Daidaita Sahu bayan ta dawo daga makaranta a kan hanyarta ta zuwa gida inda suka tafi daita.

An yi ta nema da cikiya amma sai bayan kwana 46 aka ji duriyarta, a watan Janairu ne aka gano gawar yarinyar da aka sace a ranar 4 ga watan Disambar 2021.

Yan sanda sun tono gawarta wadda ake
zargi Abdulmalik Tanko mai makarantar “Noble Kids Academy” ya binne a wani rami.

An zarge shi da hada baki da lsyaku Hashim da matarsa Fatima Jibril da laifukan da suka hada da, hada baki wajen aikata laifi da satar mutum da kuma tsare yarinyar da suka sace ba tare da
amincewarta ba da kuma kisan kai.

An kwashe kimanin watanni shida ana shari’ar wadda mai shari’a Usman Na’abba yake jagoranta.

An fara zaman kotun a karkashin mai shari’a “Usman Na’abba”, tuni aka gabatar da wadanda ake zargi su uku agaban kotun.

Barista Musa Lawan Kwamishinan Shari’a na Kano, shi ne ke jagorar lauyoyin gwamnati.

Ita kuma Barista Asiya Mohammad tana jagorantar lauyoyin dake kare Abdulmalik Tanko, da sauran mutum biyu da ake zargi da hannu akisan Hanifa Abubakar.

https://www.instagram.com/p/CgjuD94NKXJ/?igshid=YmMyMTA2M2Y=

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *