Kotu Ta yanke wa Wasu ‘yan luwadi hukuncin kisa a jahar Bauchi
An yanke wa ‘yan luwadi hukuncin kisa a Bauchi Mintuna 53 da suka wuce Wata babbar kotun shari’ar Musulunci ta yanke wa mutum uku hukuncin kisa ta hanyar jefewa, bayan ta same su da laifin yi wa wasu yara luwadi, a Ningi da ke jihar Bauchi.
Kotun ta jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya ta samu mutanen uku, da suka hada da matasa biyu da kuma wani babban mutum da ya kai sama da shekara 70 da haihuwa, da wannan laifi, wanda suka amsa. Sai dai wani jami’in kotun wand ya yi wa BBC bayani ya ce babu wani lauya da ya wakilci mutanen uku a yayin zaman shari’ar, da kotun ta yanke hukunci ranar Laraba, 29 ga watan Yuni, 2022. Kwamandan Hisbah na karamar hukumar ta Ningi, Adamu Dan Kafi, ya sheda wa BBC cewa, an kama mutanen ne a kauyen Wada a watan Mayu, bayn da suka yaudari yaran da dabino da kuma kwakwa.
Mutanen suna da damar daukaka kara cikin wata daya. Wani hukuncin a Jihar Filato A wata shari’ar kuma a jihar Filato da ke arewa maso tsakiyar Najeriya, wata babbar kotu ta yanke wa wasu mutane uku hukuncin kisa ta hanyar rataya ko allurar guba. Kotun ta same su ne da laifin kasha wani matashi ta hanyar daba masa wuka. Lamarin ya faru ne a lokacin wani sabani tsakanin matasan a lokacin bikin Kirsimeti a 2015.
Lauyan mutanen David Adudu, ya gaya wa BBC cewa ba su gamsu da hukuncin ba, wanda kotun ta yi ranar Alhamis, 30 ga watan Yuni, 2022, kuma suna shirin daukaka kara. Mutum na hudu da aka gurfanar kan laifin kisan ya rasu kafin a gama shari’ar.
Masu gabatar da kara sun bayyana gamsuwarsu da hukuncin da cewa an yi adalci. Sai dai a Najeriya ba kasafai ake aiwatar da hukuncin kisa ba, yawanci saboda batun kare hakkin dan-Adam.
maimakon haka, wadanda aka yanke wa hukuncin kisa kan zauna a gidan yari har sai abin da hali ya yi. A bisa doka, a Najeriya, sai gwamnan jihar da aka yanke hukuncin ya sanya hannu kafin a aiwatar da shi.
One comment