Saudiyya ta ba Messi jakada a fannin yawon buɗe idanu na ƙasar

Posted by

Saudiyya ta ba Messi jakada a fannin yawon buɗe idanu na ƙasar

Ministan yawon bude idanu da shakatawa na Saudiyya, Ahmed Al-Khateeb, ya sanar da cewa fitattaccen dan wasan kwallon kafar nan a duniya Loinel Messi, ya zama jakadan yawon bude idanu da shakatawa na kasar.

Messi ya samu kyakkyawar tarba a lokacin da ya isa filin jirgin saman Sarki Abdulziz da ke Jidda a ranar Litinin.

Dan wasan kwallon kafar ya samu rakiyar takwaransa Leonardo Paredes, dan waasan tsakiya na kungiyar Paris Saint-Germain da sauran abokansa.

Da yake maraba da zuwan Messi, a shafinsa na tuwita, ministan yawon bude idanun ya ce, “A yau muna maraba da zuwan Lionel Messi da abokansa zuwa Saudiyya.

Muna taya ka murnar cewa za ka ga dumbin dukiyar da ke jibge a Bahar Maliya da kuma kayayyakin tarihin da ke kasarmu.

Ba wannan ne zuwansa na farko ba, kuma ba shi ne na karshe ba, sannan ina farin cikin sanar da cewa a yanzu Messi ya zama jakadan yawon bude idanu da shakatawa a ma’aikatar yawon bude idanu ta Saudiyya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *