Yakamata Kusan Wannan Akan Case Din Tukur Mamu Da ake tuhuma da taimakawa ‘Yan Ta’adda

Posted by


ABINDA YA KAMATA KU SANI AKAN CASE DIN TUKUR MAMU

Rubutun zaiyi tsayi, amma ku daure ku karanta har karshe zaku karu Insha Allah

Da farko shi dai Tukur Mamu ya fito daga jihar Kaduna, dan jarida ne, yana da kamfanin jarida mai suna Desert Herald

Tukur Mamu shine mai taimakawa babban Malami Sheikh Dr Ahmad Gumi ta bangaren da ya shafi harkokin yada labarai, kuma duk dazukan da Dr Ahmad Gumi ya shiga neman sulhu da ‘yan ta’adda Tukur Mamu ke nadar bayanai, kuma hotunan da Tukur Mamu ya dauka na ‘yan ta’adda yana yadawa ya taimakawa hukumomin tsaron Nigeria wajen kama ‘yan ta’addan, da Tukur Mamu ya lura da hakan sai ya daina

Sunan dan jarida Tukur Mamu da kamfanin jaridarsa na Deset Herald ya fito fili ya sanu a Nigeria bayan da hadakar kungiyar ‘yan Boko Haram da fulanin jeji masu garkuwa da mutane suka tare jirgin kasa da ya kwaso fasinja daga Abuja zuwa Kaduna sukayi garkuwa da mutane

‘Yan ta’adda sun bukaci Gwamnatin Nigeria ta biya Biliyoyin Naira kafin su sake mutanen da suka kama a jirgin, amma Gwamnatin jihar Kaduna da na tarayya basu kula ba, wannan ya sa mutanen da aka kama suka nemi hanyar da ‘yan uwansu zasu kawo kudin fansa don su kubuta, hanyar kuwa itace na Tukur Mamu, daga nan ne Tukur Mamu ya zama mai shiga tsakani (Negotiator) na ‘yan ta’adda da ‘yan uwan wadanda aka kama, kuma sunansa da jaridarsa ya kara yaduwa

Akwai wadanda suka biya kudin fansa a kalla Naira Miliyan dari zuwa sama da haka, anyi kiyasi ‘yan ta’adda sun karbi kudin fansa kusan Naira biliyan 5 ta dalilin Tukur Mamu, wannan abin bai yiwa Gwamnatin Buhari da na jihar Kaduna dadi ba, domin Gwamnati ta cimma matsaya akan ba zata bada kudi ba, kuma ba zata bari a kaiwa ‘yan ta’adda kudi ba, saboda idan suka samu kudu zasu kara karfi, hakan ne ma yasa ta tura jami’an tsaro suka tare duk wata hanyar da zabi a kaiwa ‘yan ta’adda kudin fansa, to amma sai ya zamana shi Tukur Mamu ya samar da hanya ta sirrin da babu wanda ya sani sai shi sai ‘yan ta’adda

Har ila yau wannan abin da Tukur Mamu yayi bai yiwa Gwamnati dadi ba, ana nan sai ‘yan ta’adda suka nadi bidiyo kusan sai uku, suka nuna halin da mutanen da sukayi garkuwa da su suke ciki, kuma idan sun dauki bidiyon wa Tukur Mamu suke turawa bidiyon, shi kuma sai ya fitar public, hakan bai tada hankalin Gwamnati ba sai da ‘yan ta’adda suka tsara bidiyon mutanen da suka kama suna dukansu domin su ja hankali, suka turawa Tukur Mamu shi kuma ya fitar

To fitar da wannan bidiyo ya tashi hankali sosai, ‘yan Nigeria sun caccaki Gwamnatin Buhari, har sai da fadar shugaban Kasa ta fitar da sanarwa akan bidiyo, tace farfaganda ce, kuma gaskiya ne farfaganda ce, amma ba kowa zai gane ba sai wanda ya karanci makircin kidnappers, to wannan abin ya kara sa Gwamnati ta tsani Tukur Mamu, kuma wannan na daga cikin manyan dalilan da yasa aka kamashi

To sai mu duba abinda Tukur Mamu yayi bisa tsarin doka na kasa shin laifi ne?

Hakika zama mai shiga tsakanin Gwamnati da ‘yan ta’adda (Negotiator) ba laifi bane musamman akan case din da ya shafi Kidnapping, saboda muhimmancin haka har horo na musamman ake bayarwa ga Negotiator, ko ni nan Datti Assalafiy ina da shaidar zama Negotiator, don nayi course akan haka

To amma idan muka duba tsarin Negotiator irin na Tukur Mamu ta wata fuskar yaci karo da dokokin tsaron Nigeria, musamman dokar yaki da ta’addanci “Terrorism Prevention Act” da aka samar a shekarar 2011 da wanda aka sake tabbatar wa a shekarar 2013

Idan an duba wannan kudi na Terrorism Prevention Act sashi na (2) babin (d) an rubuta da turanci: “A Person or body corporate who knowingly in or outside Nigeria directly or indirectly willingly assist or facilitates the activities of persons engaged in an act of terrorism or offence under this Act” Fassaran Hausa: ” Duk wani mutumin da yana sane, kuma yana da zama a ciki ko wajen Nigeria, kai tsaye ko a fakaice ya taimaka ko ya shiga cikin ayyukan mutanen da suke aikata ta’addanci ko wani laifi dake cikin kudin dokar dakile ta’addanci”.
Idan mun fahimci abinda dokar tace to tabbas Tukur Mamu ya aikata laifin ta’addanci bisa ganganci ko neman suna, amma babu wanda yake da ikon tabbatar masa da laifi sai Kotu

Abu na gaba da ya tashi hankalin manyan maciya amanar tsaron Nigeria shine; lokacin da ‘yan ta’adda suka fasa gidan yarin Kuje dake Abuja suka kubutar da mutanen su, washegari shugaba Buhari ya ziyarci gidan yarin, kuma ya daura alhakkin harin akan ganganci na hukumomin leken asiri da bayanan sirrin tsaro, to da fadin haka sai Tukur Mamu ya saki labari cewa tun kafin ayi harin yake ta ankarar da hukumomin tsaro masu tattara bayanan sirrin tsaro amma basu kula ba, kunga anan Tukur Mamu ya tona musu asiri, dole zasu ji haushinsa, kuma karshe sune suka kamashi

Abu na gaba da ya janyo wa Tukur Mamu matsala aka kamashi shine, a sasanton da ya jagoranta da ‘yan ta’adda bai saka Gwamnati ba ma’ana hukumomin tsaro, shi yake yin komai da kansa, idan ya karbo wanda akayi garkuwa da subsai ya kira Sheikh Dr Ahma Gumi zuwa ofishinsa na kamfanin jaridar Desert Herald a dauki hoto a yada wa duniya, ya bayyana gazawar Gwamnati sannan ya tallata jaridarsa a fakaice kenan, sannan ya mayar da garkuwa da mutane a matsayin wani abinda ake yakar Gwamnatin Buhari da shi ta fuskar siyasa, kunga ba zasu kyale ba

To amma akwai wasu labarai da zaku ga ana yadawa a jaridun mutanen ‘yan Biafara cewa wai DSS ta samu Tukur Mamu da laifi dumu dumu cikin ta’addanci, an samu makudan kudin Kasashen waje da sauran kayan sojoji a gidansa, a matsayin mu na mutane masu hankali kuma masu addini ba zamu yanke hukunci akan irin wannan labarai ba, sai abinda Kotu ta tabbatar, saboda dama jaridu ne na makiyan mu wanda a kullun suke yada labarin karya da sharri a kan mu

A ra’ayi da fahimtata a matsayina na Datti Assalafiy wanda a ilmance tsaro na karanta ba zan yanke hukunci akan wannan batu ba, sai dai nace Tukur Mamu yayi kuskure ko ganganci a dalilin neman suna, kuma idan ba yafe masa akayi ba to tabbas ya taka kundin dokar Terrorism Prevention Act wanda nayi bayani a sama, Gwamnati zasu iya cin nasara kansa a gaban Alkali idan sukace ya taimaka wajen yada sakonnin ‘yan ta’adda, idan yayi da niyya mai kyau zai iya samun sassauci, amma batun wai da shi ake hada baki ake ta’addanci gaskiya ni kam ina kyautata masa zato na alheri

Daga karshe ina jawo hankalin ‘yan jarida da suke saurin yada sakonnin ‘yan ta’adda da yake kaskantar da kimar Gwamnati da kuyi hankali, akwai doka akan wannan, amma wanda ya ga zai iya don neman suna ta ya gudu ya bar Nigeria

Muna rokon Allah Ya kawo mana karshen ta’addanci a Kasarmu Nigeria

One comment

  1. Mai kake so ka isar ga jama’a? Shin ran Manu shi kadai yafi na “Yan Nigeria da ake kamawa? Sannan shi Yana da hanyar da yake samun video, da wasu bayan sirri, da taimaka musu ta wajan Kai musu kudin fansa har N5b Amma ba zai iya hada Kai da jami’an tsaro domin akamasu kokuma ayi maganinsu, wani abun sai Nigeria , adingi kokarin Kare Mai laifi, duk Mai hankali idan ya saurari wannan bayanin naka, yasan baka kaunar Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *