Ina Da Karfin Jiki, Lafiyayye Ne Ni, Tinubu Ya Warware Jita-jitar Rashin Lafiya A Bidiyo

Posted by

Ina Da Karfin Jiki, Lafiyayye Ne Ni, Tinubu Ya Warware Jita-jitar Rashin Lafiya A Bidiyo

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, daga can birnin Landan, ya shiga dandalin sada zumunta na yanar gizo ya wallafa wani bidiyonsa yana motsa jiki domin tabbatar da lafiyarsa.

A cikin wani gajeren faifan bidiyo da ya saka a daren Lahadi, an ga Tinubu akan keken motsa jiki, yana mai cewa sabanin rade-radin da ake yadawa, yana cikin koshin lafiya.

Tinubu dai ya bar Nijeriya zuwa kasar Ingila, lamarin da ya haifar da cece-ku-ce a kan cewa tafiyar tasa ba za ta rasa nasaba da rashin lafiya mai tsanani ba, musamman ma a lokacin da ya fito fili a lokacin rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da daukacin ‘yan takarar shugaban kasa da jam’iyyunsu suka yi.

Amma a cikin faifan bidiyon, wanda ya wallafa a shafin sa na Twitter da aka tabbatar, Tinubu ya kuma bar wani takaitaccen sako, yana mai cewa, “Da yawa sun ce na mutu; wasu kuma na cewa na janye daga yakin neman zaben shugaban kasa. To… a’a.

“Wannan ita ce gaskiya: Ina da ƙarfin jiki, ina cikin koshin lafiya kuma a shirye nake na bauta wa ‘yan Nijeriya tun daga ranar farko da na zama shugaban kasa.”

Sakamakon rahotannin da ake zarginsa da rashin lafiyarsa, kungiyar yakin neman zaben jam’iyyar APC ta karyata jita-jitar, tare da nuna cewa Tinubu na cikin koshin lafiya.

Da yake mayar da martani ga wani hoton bogi da ya karade kafafen sada zumunta da ke nuna cewa Tinubu ba shi da lafiya, daraktan yada labarai da wayar da kan jama’a na kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bayo Onanuga, ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa: “Ku kalli tagar gilashin sa. Bari in tabbatar wa ‘yan Nijeriya masu son sanin inda Tinubu yake. Yana Landan, a gidansa.

“Tinubu ya bar Nijeriya ne a daren ranar Asabar don hutu da kuma shirye-shiryen yakin neman zabe.

“Na gan shi na yi magana da shi sa’o’i biyu kafin ya tafi. Yana da hazaka da tausayi. lafiyarsa garau. Bai je jinyar wata cuta ba.”

Source:Amihad Media Team

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *