Mun So Mu Yi Sulhu Da Iyayen Fatima Tunda Aka Yanke Kafarta, Amma Sun Ki Ba Mu Hadin Kai, Cewar Mahaifiyar Aliyu

Posted by


Mun So Mu Yi Sulhu Da Iyayen Fatima Tunda Aka Yanke Kafarta, Amma Sun Ki Ba Mu Hadin Kai, Cewar Mahaifiyar Aliyu

… ta kuma nemi dangin Fatima su yafe ma Aliyu.

Wata ɗaya da samun rahoton yanke kafar Ɗaliba Fatima a lokacin murnar kammala jarabawar NECO ga ɗalibban makarantar Kalipha International Secondary School a jihar Sokoto, an lashe wata ɗaya cif ana kai ruwa rana tsakanin dangin Fatima da dangin Aliyu wanda ya bige Fatima har Saida aka yanke ƙafarta.

Rahoton da muka samu daga muryar mamar Fatima Hajiya Hadiza, ta bayyana cewa babu Maganar yafiya. Koda Sama da kasa za su haɗe ba za su yafe ba sai an biya su Diyyar ƙafar Fatima. “Kuɗi Sunci Bura’ubansu”

A wata tattaunawa da tawagar manema labarai suka yi a Sakkwato ciki har da wakilin mu, da mai baiwa Gwamna Tambuwal shawara a kan Hakkin Bil’adama Hon. Hajiya Ubaida Bello, ta shaida mana cewa a cikin zaman Sulhu da suka yi da Iyayen Fatima, Iyayen Aliyu da Jami’ai na Human Rights, “mun tashi babu daɗin rai, domin Mahaifin Fatima ya gaya muna maganganu marasa dadi a idon mu.

Ya kuma tabbatar muna da cewa shi ba zai sulhunta da kowa ba sai dai a biya shi diyyar kafar ‘yar shi da kuma diyyar ɓacin ran ta na har iyakar rayuwar ta” in ji Hon. Ubaida.

A lokacin da muka yi zama da Mamar Yaron tare da manema labarai, Mahaifiyar cikin muryar tausayi ta shaida mana cewa “mun bi duk hanyar da za’abi wurin ganin an samu sulhu tsakanin nu da dangin Fatima tun farkon lokacin da abun ya faru zuwa yanzu, amma dangin Fatima ba su aminta a yi Sulhun ba”

Ta kara da cewa “Mun ba da duk abin da ake bukata ga lafiyar Fatima ba tare da kasawa Ko gajiyawa ba, amma iyayen basu hakura ba, Mun shaida musu mun ɗauki nauyin komai na Jinyar Fatima har zuwa samun Sauki da Yi mata kafar roba amma basu hakura ba”.

“A duk lokacin da na je asibiti domin duba Fatima hantara ta ake yi na rasa bacci da cin abinci saboda yanayin Fatima inji Mamar Aliyu.

Mamar ta kara da cewa tafi tausayin yanayin Fatima da’aka yankewa kafa take fama da jinya asibiti fiye da Ɗanta Aliyu dake zaman gidan kaso tsawon wata ɗaya Ahalin yanzu.

A daidai Lokacin da wasu ke tausaya wa Fatima, wasu Mutanen ma suna tausayawa Aliyu zaman shi karamin yaro a kurkuku cikin mnyan barayi da masu manyan laifukka, garkuwa da mutane da Mashaya, Mahaukata da Mutane Masu hatsarin gaske. Abin da wasu ke masu sharhi ke bayyana fargabar zaman sa gidan kaso ya zama silar sauyawar rayuwar sa zuwa wani Mutum na daban achikin al’umma.

Mamar Aliyu ta rufe magana cikin kuka da zubda hawaye tana cewa wannan kaddara che daga Allah muna rokon a yi hakuri a yafe mana! Wannan labarin de ya dauki hankalin kafafen sadarwar zamani inda kowa ke fadin albarkacin bakin sa, abin da ake ganin akwai bukatar samun sun hu tsakanin bangarorin biyu, abin da bangaren mahaifan yaro suke nema, yayin da ban garen mahaifin fatimar ya ce Ai bau

Source:Muryar ‘Yanci

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *