YA CANZA ADDINI SABODA KUNCIN RAYUWA
Daga Dattyassalafy
حسبنا الله ونعم الوكيل
Wannan matashi Musulmi ne sunansa Yusuf Adam, ya fito daga garin Birnin Gwari a Jihar Kaduna
Allah Ya aiko masa da jarrabawan rayuwa ya shiga cikin kunci, da ya rasa mafita sai yayi riddah saboda an yaudareshi da wasu ‘yan kudade
Ya bar gurin iyayensa a Birnin Gwari ya koma gurin wadanda suka canza masa addini a jihar Taraba, yanzu haka yana can a Taraba
Kafin ya canza addini, masu garkuwa da mutane sun taba kamashi, mahaifinsa ya hada kudi Naira Miliyan 5 ya kubutar dashi
Yanzu haka matashin yana nan a Facebook har posting yake yi yana bayyana farin cikinsa da yin riddah
‘Yan uwansa sun bukaci a tayasu da addu’ah Allah Ya dawo da hankalinsa cikin Musulunci
kada kumanta kudinga muna share na post inmu zuwa ga abokaninku domin bamu qwarin guiwar kawomaku ingantattin sahihun labaran duniya a cikin harshen hausa dana turanci mungode da ziyartar shafin KuryaLoaded.ng dakunkayi
Idan kuna da tambaya ko wani labari da kuke son sanar da mu, ko tallata hajar ku kuna iya aika mana da sako a shafinmu na Facebook, ko tura sako a number admins dinmu +23408141702912