Innalillahi Wainna Ilaihi Raji'un: An kama wasu 'yan luwadi 5 Sun yi ma dan shekara 20 fyade a Kano

Bidiyo YANZUN YANZUN: Yan sanda sun kama wasu ‘yan luwadi 5 da suka yi ma wani dan shekara 20 fyade a Kano

Posted by

Yan sanda sun kama wasu ‘yan luwadi 5 da ake zargi da laifin yin ma wani dan shekara 20 fyade a Kano.

Matashin da aka yi ma fyaden ya ce wadanda ake zargin sun yaudare shi zuwa wurare daban-daban inda suka yi lalata da shi sau da yawa

Kalli Bidiyon anan:

Innalillahi Wainna Ilaihi Raji'un: An kama wasu 'yan luwadi 5 Sun yi ma dan shekara 20 fyade a Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wasu ‘yan luwadi biyar da ake zargi da yi wa wani matashi dan shekara 20 fyade, Tajudeen Hashim, a karamar hukumar Gwale da ke jihar Kano.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, ya ce an kama su ne bayan da kanwar wadda aka yi wa fyaden ta kai rahoto ga ‘yan sanda.

Innalillahi Wainna Ilaihi Raji’un: ‘Yan sanda sun kama wasu ‘yan luwadi 5 da suka yi ma wani dan shekara 20 fyade a Kano

A cewarsa, wadanda ake zargin sun kai matashin wanda suka yi ma fyadenne zuwa wurare daban-daban inda suka yi lalata da shi mai yawa, wanda hakan ya haifar masa da ciwon ciki mai tsanani.

“A ranar 15/07/ da misalin karfe 5:00 na yamma, wata mata da ke garin Mandawari Quarters, karamar hukumar Gwale, jihar Kano ta shigar da korafin cewa dan uwanta mai suna Tajuddeen Hashim, mai shekaru 20 da haihuwa, ya ce mata cikinsa yana tsananin ciwo da zafi,” in ji Kiyawa.

Abdullahi Haruna Kiyawe

“Da ake yi masa tambayoyi, ya bayyana cewa wadannan mutanen guda 5 suka yaudare shi da cewar za su bashi makudan kudade, suna kaishi wurare daban-daban kana suka yi lalata dashi a lokuta mabanbanta. Mutanen sun hada da:

  1. Ahmed Inuwa, shekaru 34, na Sharada Quarters, Kano Municipal LGA, Kano
  2. Nasiru Isyaku Mohd, dan shekara 48, daga Diso Quarters , Gwale LGA Kano
  3. Lawan Uba, mai shekaru 31 wanda yake Kofar Dan Agundi Quarters, Kano Municipal LGA
  4. Auwalu Uba, shi kuma mai shekaru 40 da haihuwa dake Mandawari Quarters, Gwale LGA Kano, da na biyar dinsu
  5. Rabiu Sharu, mai shekaru 33 a Kabuga Quarters, karamar hukumar Gwale, Kano,

Yace sun yaudare shi zuwa wurare daban-daban tare da yin lalata da shi a lokuta da dama, a sakamakon haka, ya sami mummunan ciwon ciki.

“Bayan samun rahoton an garzaya da matashin da aka yi ma fyaden zuwa asibitin koyarwa na Muhammadu Abdullahi Wase dake nan Kano inda aka yi masa jinya aka sallame shi, Nan take kuma kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, fsi ya tashi tawagarbjami’ansa tare da ba shi umarnin kamo masu laifin cikin sa’o’i 48.

“Nan take rundunar ta damko dukkanin mutane biyar (5) da ake tuhuman a ranar 16/07/, wato sa’o’i 24 bayan rahoton.

A binciken farko, duk wadanda ake zargin sun amsa laifinsu. “Daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Rabi’u Sharu mai shekaru 33 a unguwar Kabara Quarters Kano, ya kara da cewa shi ne mutum na farko da ya fara yaudarar matashin kuma ya yi lalata da shi.

Kiyawa ya kara da cewa, “Ana ci gaba da bincike don gano gaskiyar lamarin kuma za a gurfanar da duk wadanda ake tuhuma a gaban kotu bayan an kammala binciken.

One comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *