Yadda Wani matashi ya Auri Mahaifiyarshi

Posted by

Duniyar nan dai cike take labarai kuma idan har da sauran numfashin ka, to fa tabbas baka gama gani ko jin abun al’ajabi ba daga ko’ina daga fadin duniya.

Wani labari mai kama da almara da ya girgiza duniya shine na wata mata yar kasar Malawi dake a nahiyar Afrika da ta auri dan ta mai shekaru 30 a duniya har ma kuma da bayyana dalilin ta na yin hakan.

Matar dai mai suna Memory Njamani wadda ke da shekaru 47 a duniya na bayyana cewa ta yanke shawarar auren dan na ta ne biyo bayan wani dogon nazari da tayi akan irin wahalar da ta sha wajen dawainiya da shi har ya zama mutum.

Matar ta kara da cewa a don haka ne ma dai ta yanke shawarar cewa gaskiya ba za ta bari wata can ta mori dan na ta ba kara ita ta aure abin ta.

Memory Njamani dai ta kara da cewa duba da irin wahalhalun da ta sha akan dan nata tun daga raino da tarbiyya har zuwa ilimin sa, ta yanke shawarar cewa ita zata aure kayan ta.

Source:Amihad.Com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *