Zaurukkan ilimin addinin Musulunci Ga Kasar Hausa
A Kasar Hausa akwai Malamai Dattijai, da ke fitowa da la’asar sakaliya, galibi a kofar gidajensu, ko a cikin masallatai, Almajirai na zuwa kowa ya sanya littafi ya dauki karatu. Musamman littafan Mazhabin Fikihun Malikiyya.
Wasu lokutan a kan yi wadannan majalisai bayan sallar asubahi har zuwa lokacin hantsi, wasu bayan sallar isha’i. Wasu malaman masu himma kuwa sukan had’a mabanbantan lokuta, su yi da safe, da rana, da yamma, da dare.
Galibi irin wadannan malamai za ka samu dattijai ne, shekarunsu sun ja, an manyanta. Ba su cika damuwa da abinci ba sai dan farau-farau na kunu, ko butar ruwa da ke gefensu suna dan guntsa lokaci, lokaci. Haka nan abin duniya bai dame su ba, suna rayuwa matsakaiciya. Basu fiye fita ko ina ba, in banda salla, da jana’iza, da zumuncin da ya kama.
Sannu a hankali malaman na tafiya, wadannan zauruka na dusashewa. Allah ka yi Rahama ga Mazan jiya, ka kyautata sha’anin na baya.
Mai karatu, ko za ka ambato mana wani cikin irin wadannan malamai a garinku, wadanda ke zama a kofar gidajensu, ko a masallatai bayan la’asar su bayar da karatu.
Musa Muhammad Dankwano.
One comment