Shi dai Sheikh Adil ‘al-Kalbani, an haife shi ne a birnin Riyadh na kasar Saudiyya, a ranar 4 ga watan Afrilun shekarar 1958 – wanda yayi dai-dai da watan Ramadan a wancan lokacin – kimanin shekaru 64 ke nan yanzu.
Asalin iyayen Sheikh Adil ‘al-Kalbani yan gudun Hijrah ne daga garin Ras Al-Khaimah na Hadaddiyar Daular Larabawa – kuma sun shiga kasar Saudiyya ne a shekarar 1950.
An ruwaito cewa sabida rashin karfi da iyayen sa suke dashi a lokacin, Sheikh Adil ‘al-Kalbani ya kasance ma’aikaci a gwamnatin kasar Saudiyya a matsayin Akawu I inda daga bisani kuma ya kama aiki da Ma’aikatar Kula da Zirga-zirgar Jirage ta Kasar Saudiyya, jim kadan bayan ya kammala karatunsa nag aba da Sakandare – har ma ya fara halartar Jami’ar Sarki Sa’ud na Saudiyya.
Malamin Adil ‘al-Kalbani na farko a fannin Addinin Islama, shine Hasan ibn Gaanim al-Gaanim – inda ya karanci littafan Sahih al-Bukhari, Jami` at-Tirmidhi da kuma littafin ilimin tafsiri na Ibn Kathir duka a wurin sa.
Haka nan, Sheikh Adil ‘al-Kalbani, ya karanci ilimin tafsiri na littafin Al-Baydawi a wurin malaminsa, Sheikh Mustapha Muslim a Jami’ar Musulunci ta Imam Muhammad Ibn Sa’ud – daga nan kuma Sheikh Adil ‘al-Kalbani ya karanta littafin Akhir Tadmariyah a wurin Malam Abdullah Ibn Jibreen – ya kuma koyi karatun Al-Qur’ani Mai Tsarki a wurin Sheikh Ahmad Mustafa.
Sheikh Adil ‘al-Kalbani ya samu nasarar hayewa jarabawar da kasar Saudiyya take yiwa malamai domin zama limamai ne, tun a shekarar 1994 – inda yaci jarabawar da gagarumar nasara; kuma aka dauke shi a matsayin limami a wani masallaci daje cikin filin sauka da tashin jirage na birnin Riyadh.
Kwarewarsa A Fagen Limanci
Bayan Sheikh Adil ‘al-Kalbani ya dauki lokaci yana limanci a filin sauka da tashin jirage na Riyadh din ne, sai kuma likafarsa taci gaba, inda ya koma babban masallacin Sarki Khalid da aikin nasa na limanci.
Tun asali dama, Sheikh Adil ‘al-Kalbani, mutum ne da ya dade yana burin ya kasance daya daga cikin manyan limaman Masallacin Harami na Makkah – kuma cikin shekaru biyu kacal, cikin ikon Allah, sai Sarki Abdullah na Saudiyya, ya neme shi daya jagoranci Sallar Tarawi a Masallacin Haramin a shekarar 2008.
Haka nan, Sheikh Adil ‘al-Kalbani ya ziyarci cibiyar horarwa akan ilimin Al-Qur’ani ta Minhaj ‘ul-Qur’an ta kasar Japan dake birnin Bandu a ranar 30 ga watan Yunin shekarar 2013.
Amma duk da irin wadannan karance-karancen da Malam Adil ‘al-Kalbani yayi, kullum yakan cewa shi ba Malami bane; shi makarancin Al-Qur’ani ne kawai.
Rayuwar Sheikh Adil ‘al-Kalbani
Sheikh Adil ‘al-Kalbani magidanci ne; yana da mata biyu – kuma Allah Ya albarkace shi da yaya har goma-sha-biyu (12).
Faduwar Na’urar Gini A Makkah
A lokacin da wata na’uarar gini ta fado a cikin Masallacin Harami – a dai-dai lokacin da ake gudanar wani aikin Hajji – wanda har al’uma da dama aka ruwaito cewa sun rasa rayukan su, sai Sheikh Adil ‘al-Kalbani ya rera wata wakar fasaha – wadda a cikin ta yake kalubalantar abinda ya faru, har ta kai ga wannan karfen ya fado akan mutane.
A cikin wakar ta sa, Sheikh Adil ‘al-Kalbani yace “abu ya fado kasa kan mutane – ana tsaka da Sallah…hakika wannan ba karamin sakarci bane.”
A cikin wakar, sai ya kara da cewa “…amma sauran karafunan da basu fadowa ba; hakika sun nuna halacci da kyawun kai.”
Akidar Sheikh Adil ‘al-Kalbani
Akan batun irin akidar da Sheikh Adil ‘al-Kalbani, akwai wadanda suke ganin kamar tsaurin ta sa akidar yana shige data yan kungiyar ISIL.
Rarrabewa Tsakanin Maza Da Mata A Masallaci
Yana daga cikin abubuwan da Sheikh Adil ‘al-Kalbaniyayi wadanda suka tunzura gwamnatin kasar Saudiyya, har daga karshe aka dauki nauyin sauke hi daga mukamin limanci; irin kalubalantar doka ko tsarin rarraba mata da maza da ake yi a Masallacin Harami – inda yace “ana yiwa mata taware – da kuma barin sus u kadai” sai dai kawai a rika mu’amala dasu ne kawai ta hanyar yin amfani da na’urar amon-sauti – har ma yace “wannan ba komai bane sai tsoron mata.”
Alakar Sheikh Adil ‘al-Kalbani Da Shi’a
A wata hira da Sheikh Adil ‘al-Kalbani yayi da kafar yada labarai ta BBC tayi dashi, ya yi Magana akan Shi’a, inda ya nuna kamar ta halatta – a’amarin daya tunzura masoyansa a kasar Saudiyya.
A shekarar 2019, hakanan, Sheikh Adil ‘al-Kalbani ya janye kalamansa akan maganar da yayi dangane da Shi’a – har ma ya dogara da wani littafi na wani malami Hatim al-Awni.
Alakar Sheikh Adil ‘al-Kalbani Da Kade-Kade
A cikin wata fatwah da Sheikh Adil ‘al-Kalbani ya taba bayar wa a shekarar 2010, ya ce kida abu ne wanda ya halatta a Musulunci.
A shekarar 2019, haka nan, malam ya sake yin Magana akan fatawar sa akan kida – inda ya sake cewa ya halatta.
Tirkashi Wani Tsoho Ya Auri Jikanyarsa Yaki Kuma Yarda Ya Sake Ta A Garin Tsafe
A shekarar 2021 cikin watan Nuwamba ne kuma, aka gano Malam cikin wani fai-fan bidiyon fim mai dogon zango mai suna Combat Field – Riyadh Season 2021.
Jan Hankali Game Da Rayuwar Sheikh Adil ‘al-Kalbani
Mutane da dama yanzu, sun duƙufa wajen yayata maganganu akan yadda rayuwar Sheikh Adil ‘al-Kalbani ta sauya – sakamakon tajriba daya samu a rayuwa – wanda ba bu wani mutum daya wuce fadawa cikin ta. Abin takaici ma, har wadansu mutanen ma, sukan wuce gona da iri; su riƙa ƙoƙarin ayyana shi a matsayin batacce ko wanda ya tabe; yabi Shaydan.
Kuma har yanzu, duk da irin faya-fayen bidiyon da ake ta yadawa na Sheikh Adil ‘al-Kalbani yana fim; ko yana cikin ruwa; ko wani abu. Ba bu wani hoto da za’a iya nuna wa na sa, tare da mace suna masha’a.
Abinda na lura shine, wadansu mutanen kamar jin dadin yada labaran Sheikh Adil ‘al-Kalbani ne – kamar su ba sa aikata laifi. A yiwa Malam addu’a; mu yiwa kan mu addu’a; mu yiwa junan mu addu’a. Allah Ya Shiryar Damu!
SARKIN KANO YA NAƊA KALIFAN MUHAMMADU SUNUSI NA ƊAYA.
One comment