Jarumar shirin Dadin kowa Sarah Aloysious wacce aka fi sani da Stephanie ta bayyana a cikin wata bidiyo tana karin bayani akan wakar yabon Manzon Allah S.A.W da tayi.
Kamar yadda kuka sani jarumar Stephanie a kwanakin baya tayi waken yabon Fiyayyan halitta Annabi Muhammad S.A.W, inda jama’a sukayi ta cece-kuce a kai wasu ma mata fatan alkairi wasu kuma akasin haka.
Tun bayan bayyanar wata bidiyo wanda aka ga jaruma Stephanie a ciki tayi shiga irin ta ‘yayan Musulmai tana rera wakar yabon Fiyayyan halitta Annabi Muhammad S.A.W,.
Tun daga wannan lokacin jama’a suka fara cece-kuce da fadin maganganu kala-kala akan jarumar inda wasu suke zaton jaruma Stephanie tayi hakan ne domin neman suna a wajan al’ummar Musulmai mabiyanta.
Sannan kuma wasu suna tunanin jarumar tayi hakan ne domin tama sha’awar addinin Musulinci, amma sai mukaga jarumar ta bayyana a cikin wata bidiyo wanda shafin VOA dake kan manhajar Facebook suka wallafa.
Jarumar take cewa: Kai musulmi ni kirista ce, ban tashi na roki Allah don yayi ni a kirista ba, haka zalika kai ma musulmi ba ka tashi ka roki Allah yayi ka a musulmi ba.
Sannan ta kara da cewa: kawai wayar gari kowa yayi ya gan shi da addinin sa, tace ta na matukar jin takaici idan taga musulmi ko kirista yana zagin wanda suke da bambancin addini da shi.
[tie_list type=”checklist”][/tie_list]
Jaruma Stephanie tace: kowa nata ne kuma duk wanda zai sota ya sota yadda ta ke, sannan ta musanta batun cewa tayi wakar yabon manzon Allah ne don tana so ta musulunta, tace kawai ta na son kowa ne.
[ads1]
Har kawo yanzu jarumar ta musanta zargin da ake yi mata na neman jan hankalin jama’a ta hanyar yin wakar yabon Manzon Allah S.A.W, Inda tace sam ba haka ba ne.
Inda cewa tana son kowa ne ba don addinin sa ba don haka itama take son a sota a yadda ta ke.
Ga bidiyon nan domin ku kalla kuji cikekken bayani daga bakin jaruma Stephanie.
One comment