ABIN TAUSAYI: Wata budurwa ta shafe shekaru 19 bata iya ko rarrafe, saidai a dauke ta cikin Bahon roba

Posted by


Abin tausayi da jejeto da ya sami wata matashiya ya tada hankalin mutane. Ta rasa komi nata tun tana karamar yarinya bata iya tafiya balle iya sarrafa kanta ko ayyukan yau da kullum.

Wata matashiya da aka haife ta a 1996 zuwa 1997 har kawo yanzu a cikin bahon roba ake saka ta, hakan ya samo asali ne na rashin lafiyar ta tun tana karama

Matashiyar, mai suna Rahama Haruna an haife ta a jihar Kano, dake arewacin Najeriya. Zuwa yanzu tana da shekaru 25,  Saidai wata majiya ta bayyana cewa; kafafu da hannayen Rahama sun daina girma ne yayin da ta kai shekaru 6 a duniya. Kamar yadda wata kafar Online ta rawaito.

Hotunan da wani shahararren madaukin hoto, Maigatanga ya wallafa sun yi ta yawo a kafafen sada zumunta, lamarin da ya saka mutane da dama zubda kwalla.

An bayyana Rahama ta gamu da ciwon shanyewar gabobi ne, cutar da aka kasa gano irinta tun yarinta. Maganar da ake kawo yanzu ko rarrafe bata iya yi balle tafiya, saidai a dauke ta cikin baho.

kada kumanta kudinga muna share na post inmu zuwa ga abokaninku domin bamu qwarin guiwar kawomaku ingantattin sahihun labaran duniya a cikin harshen hausa dana turanci mungode da ziyartar shafin KuryaLoaded.ng dakunkayi

Idan kuna da tambaya ko wani labari da kuke son sanar da mu, ko tallata hajar ku kuna iya aika mana da sako a shafinmu na Facebook, ko tura sako a number admins dinmu +23408141702912

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *