Shirin ALAQA Na Season Two Episode Ten Ya Karkatane Akan Abubuwa Guda Uku
NA FARKO SHINE:
Yanda Ake Neman Aure A Musulunci.
Sau Da Yawa Mafi Akasarin Auren Da Akeyi A Wannan Zamanin Ya Sa6a Da Yadda Addini Ya Tanadar Sakamakon Zamani Yazo Da Inde Saurayi Da Budurwa Sun Daidaita Tsakaninsu Kawai Sai A Fara Maganar Aure.
A Addinance Musulunci Ya Gindaya Mana Yanda Zamu Fara Neman Aure Tun Daga Matakin Neman Auren Har Izuwa Yanda Za’ayi Auren, Musulunci Ta Fadi Yanda Hakan Zai Kasance.
Kamar Yanda Yake Faruwa Acikin Shirin ALAQA Yana Kara Tunatarwa Mutane Kan Cewa Idan Mutum Zaiyi Aure Anaso Yayi Bincike Mai Zurfi Domin Za6ar Mata Ta Gari Mai Tarbiya Kuma Daga Gidan Mutunci, Hakan Yana Daya Daga Cikin Dalilan Da Yake Sa Aure Yayi Armashi Kuma Asamu Zuri’a Ta Gari.
Kamar Yanda Aka Fara Binciken HALISA A Farko Wanda Aka Tura Nasiru Yayi Bayan Ya Samu Kyakkyawan Sakamako Daga Baya Kudi Yasa Ya Canza Sakamakon Daga Mai Kyau Zuwa Mara Kyau.
Yana Da Kyau Ayi Bincike Mai Zurfi Domin Tabbatar Da Ingancin Sakamakon, Kamar Yanda ALHAJI LAWAN Yayi Bayan Nasiru Ya Kawo Masa Sakamakon Farko Wanda Shi Da Yayi Nashi Binciken Tasha Bambam Da Wanda Nasiru Ya Kawo Mishi.
Yana Dakyau Iyaye Su Dauki Darasi A Wannan Shiri Musamman Yanda Sakamakon Binciken Nan Yazo Guda Biyu Daban-Daban Domin Shi Maganar Aure Abu Ne Wanda Za’a Gina Rayuwar Ma’aurata Harma Da Zuri’ar Da Zasu So Bayan Auren.
NA BIYU SHINE:
Dolene Iyaye Su Bawa ‘Ya’yansu Ingantaccen Rayuwa Da Tarbiya Domin Sauke Nauyin Da Allah Ya Basu, Wanda Rashin Yin Hakan Na Iya Samar Da Gur6ataccen Ahali Sannan Da Fadawa Fushin Ubangiji.
MISALI
Kamar Dai Yanda Ya Bayyana Acikin Shirin ALAQA Ta Tabbata HALISA Mutuniyar Kirkice Ta Samu Shaida Awajen Al’umma Kan Cewa Ita Din Yar Gidan Mutunci Ne Mahaifinta Ya Bata Tarbiya Daidai Gwargwado Wanda Dukda Mahaifinta Ya Rasu Hakan Baisa Ta Kauce Akan Tafarkin Da Ya Daura Taba
NA UKU SHINE:
Kamar Yanda HALISA Ta Samu Tarbiya Ingantacce Hakan Baisa Tarbiyarta Ya Samu Rauni A Yayin Da Tayi Zurfi A Karatunta Na Zamani Ba. Hakan Na Nufin Duk Tarbiyar Da Yarinyar Ta Samu Matukar Zataji Tsoron Allah Ta Kare Mutuncin Kanta Da Ikon Allah Babu Irin Karatun Da Zaisa Tarbiyarta Ya Samu Rauni.