Abinda Yakamata Kusani Dangane da Siyarda Tsoffin Facebook Pages da akeyi

Posted by

SHIN ME AKE YI DA PAGES MARASA LIKES DA AKE SAYA?

Mutane da yawa su na min wannan tambayar wai “Me ake yi da pages din in an saya”

A yau ga amsarku game da wannan tambaya. Ana yin abubuwa da wadannan pages ne idan an saya kamar haka:

1. a. Ana saya a sayar – Wassu su na saya ne su sayar da shi a basu riba. Nima ina irin wannan.

b. Wassu su na sayar da shi ga wadanda su ke zaune a kasashen da ake iya amfani da pages wajen tsarin talla na Facebook da su ke biya (In-Stream video adds) don suma su ci riba.

2. a. Ana amfani da shi a matsayin personal page – Wassu su kan sayi irin su su maida su page nasu na musamman don posting wani abun da ya jibamce su ko ya jibanci kasuwancin su.

b. Wassu suna gina page din su sayar da shi.

3. Don dora tallan Facebook (Facebook adds) – Wassu su na sayan pages din ne don su na amfani da su wajen tallata kasuwancinsu a irin pages din ta hanyar talla na Facebook.

4. Insta article/In-stream adds – Wassu su na amfani da shi wajen sarrafashi ta hanyar amfani da shi don wani tsari da Facebook ya bada dama publishers su ke yi mai suna insta article.

sannan wassu pages din kamar ana amfani da su wajen ginasu a nemi talle da Facebook ke saka ma kowanne video kamar yadda tsarin YouTube ya ke, ana kiransa da suna In-Stream video. Wannan Tsari shi bai fara cikakken aiki a nan kasar Nigeria ba. Amma masu sayan page din suna iya amfani da shi ta hanyar amfani da wassu yan’uwa da abokai da su ke a wassu kasashe don gina shafuka da samun wannan tsari na in-Stream video adds.

wadannan kenan.

AMMA ME YA SA SAI TSHON PAGE?

Amsa: Ana sayan tsoffin pages din ne ana amfani d su wajen yin dukkan wadannan abubuwa da na lissafo a sama sabi da Facebook ba su fiye block din tsoffin pages ba. Ka kuwa ba za ka so ka gama gina page za ka data samun kudi ba, ko ka gama sayan pages Facebook su yi block dinsa ka ga ba karamar hasara kai ba.

Allah ya sa mu dace.

In ka na da wata tambaya ajiye min ita a kasan comment idan na sani na baka amsa insha Allahu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *