An Gano Kwarangwal Din Wani Magidanci A Dakinsa Shekaransa 4 Da Mutuwa Ba A Sani Ba
Al’ummar Adeosun/Idi Orogbo da ke karamar hukumar Ido a jihar Oyo sun shiga cikin rudani a ranar Lahadin da ta gabata, bayan da suka gano wani mai gidansu Mista John Aderemi Abiola a dakinsa, kusan shekaru hudu da ganinsa na karshe a watan Disambar 2018.
An gano hakan ne bayan da al’ummar yankin suka yanke shawarar shiga gidan nasa, tare da amincewar hukumar ‘yan sanda, domin share dajin da ke cikin gidansa da ya mamaye katangarsa zuwa gida na gaba.
Yayin da shekarar 2019 ta shiga cikin 2020, mazauna garin sun fara tunanin inda mutumin zai kasance tun bacewarsa.
Ko da yake an bayyana wasu biyu daga cikin wadanda ya saba tattaunawa da su cewa ya yi niyyar zuwa Fatakwal, Jihar Ribas, amma da aka tuntubi wadanda suka je wajen bikin Ileya din sun ce basu gan shi ba a wajen bikin.
Daga nan ne ya sa suka yi tunanin ya tsaya ne a can. Jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito cewa kiran da ake yi a layukan wayarsa ba sa shiga.
Bayan da aka lura ciyawar da ke harabar gidansa ta yi yawa, sai masu gidajen unguwar suka yanke shawara a wani taro domin lalubo hanyar shiga harabar gidan nasa domin share daji.
Daga nan zuwa shekarar 2021, har zuwa shekarar 2022, mazauna unguwar da ba su san inda yake ba, suka sake yanke shawarar su je su sake share dajin.
An ruwaito cewa leburori da suka je share daji sun lura da cewa tagar dakin Mista Abiola a bude take, kuma motarsa kirar Volkswagen na lullube da ciyawar haraban wanda hakan ya sa aka fara neman sanin mene ke faruwa.
Ko da suka kitsa kai cikin gidannasa bayan sun balle kofar shiga gidan sai suka taras da kwarangwal dinsa a kan gadonsa.
Lamarin ya tayar masu da hankali inda suka razana sannan nemi hanyar guduwa, amma daga bisani wadansu suka yi karfin halin tsayawa su gane ma idanunsu karahen gani.
Da suka gudanar da bincike sai suka gano cewar lallai wannan mutumin nan ne da ya bace shekaru 4 baya ashe ya mutu ne babu wanda ya sani.
Allah ya jikan musulmi.
kada kumanta kudinga muna share na post inmu zuwa ga abokaninku domin bamu qwarin guiwar kawomaku ingantattin sahihun labaran duniya a cikin harshen hausa dana turanci mungode da ziyartar shafin KuryaLoaded.ng dakunkayi
Idan kuna da tambaya ko wani labari da kuke son sanar da mu, ko tallata hajar ku kuna iya aika mana da sako a shafinmu na Facebook, ko tura sako a number admins dinmu +23408141702912