Jarumin kannywood Aminu Sharif momo ya bayyana cewa” Ba Laifi Bane Don Anyi Min Barna Nace A Biya Ni, Koni Nayiwa Mutum Barna Zan Biya Shi.
Don Haka Ina Mamakin Mutanen Da Suke Shiga Abubuwan Da babu Ruwansu” a ciki cewar’ jarumin masana’antar kannywood Aminu Shariff momo.
Martanin Jarumin Finafinan Hausa, Aminu Sharif Momoh Ga Masu Kalubalantarsa A Wani Bidiyo Da Aka Nuno a shafin sada zumunta.
Yayin da Wani Dan Ga Ruwa Ya Biya Shi Kudi kimanin naira duba (10) sakamakon Gogar Masa Mota Dayayi a cikin kasuwar Singa dake jihar Kano.
Aminu Sharif momo tuni yace sai anbiya shi kudin gyaran motar sa, da akayi masa barna, yayin da wasu suke ganin yafi karfin abun domin bai kamata yace sai anbiya shiba.
Jarumin yayi allah wadai da wasu mutane da sukeyi masa ihu, a wurin sakamakon karbar naira dubu goma da yayi a wannan lokaci har takai ga anyi masa video, ana yadawa a shafukan sada zumunta.
Kuci gaba da kasancewa da shafin Janzakitv, domin kawo muku ingantattun labaran abubuwan da suke faruwa a duniya baki daya mungode.