Advertisement

Murja Ibrahim Kunya Ta Sha Girgije Ta Sha Rawa a Sabon Videon Umar M. Sharif

Posted by

Kai Jama’a! Wai shin Murja Ibrabim Kunya ce?!!!!!!!

Advertisement

Ku tayamu kallo, shin wai wannan watannan shahararriyar ‘yar tiktok dinnanne Murja Ibrahim Kunya ce?

To fa lallai Murja Ibrahim Kunya ta shigo gari, domin idan mai karatu bai mance ba, Murjan ta kasance mai farin jini a kafan sada zumunta na tik-tok inda take antayo ma mabiyanta kayatattun abubuwa masu jan hankali na barkwanci.

Murjan dai Allah yayi mata wata irin baiwa na surutu, kalamai wasu na bin wasu, kana ga saurin zance. Kalaman kuwa ko da ma’ana ko babu.

Advertisement

Hakika tana nishadantar da ‘yan tik-tok, musamman mazaje da takwarorinta mata.

Murja dai ‘yar talakawa ce kuma mai tutiya da alfahari da asalinta da gidansu. Bata kyamar talaka ko karyan wadata ko boye asalinta, hakan yasa tayi farin jini a kafofin sada zumunta.

Ana haka, kwatsam sai muka tsinci Murjan cikin wata ta Umar M. Sharif da wani ya hau kan wakan.

Advertisement

Ku kalli wakan:

Umar M Sharif (MURMUSHI A DO NA FUSKA) ft Danfulani original latest video.

Ita dai Murjan ba a santa a Kannywood ba sai a tiktok, shi yasa abin ya baiwa mutane mamaki, to amma ba abin mamaki bane saboda Tik-tok da Kannywood kamar dan jumma ne da dan jummai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *