Innalillahi Wa’Inna”ilaihi Raji’un Wasu Yan Bindiga Sun Kashe Wani Babban Barrister A Jihar Zamfara

Posted by

Kwana Ukku Zuwa Hudu Dasuka Gabatane Wasu ‘yan ta’adda suka kashe wani Bairster Lawyer A Garin Gusau Kamaryanda Majiyarmu tasamu A wani Rahoto Damuka Gani Kamar Haka

‘Yan Bindiga Sun Kashe Babban Lauya A Daren Jiya A Garin Gusau

Rahotanni sun nuna cewa marigayin mai suna B.T Aza ya ga ‘yan bindigan ne a lokacin da yake kokarin shiga gidansa, sai ya yanke shawarar ya juya, amma suka bi shi suka harbe shi har lahira.

Barrister ya kasance yana daya daga cikin manyan lauyoyi a jihar ta Zamfara, kuma shine shugaban B.T Aza & C,o chambers.

Sun harbe shi ne a kusa da gidansa dake bayan hedikwatar hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) akan hanyar komawa gida ta Bye pass dake Gusau a unguwar Saminaka.

Wannan lamari daya faru yayi matukar tayarwa da al’ummar unguwar hankali bisa ganin yadda aka kashe, hazikin lauyan mai gaskiya da taimakon al’ummar yankin nasa.

Hakika anyi babban rashin kwararren lauyan gwamnatin jihar ta zamfara dake garin Gusau, saidai majiyar mu ta samu labarin cewa’ batun yau ba ake bibiyar sa.

Ganin yadda mutumin ya rike aikinsa da gaskiya da kuma taimakawa al’umma hakan yasa wasu daga cikin mutanan basa son, abinda yake har takai ga sun kashe shi.

Kuci gaba da kasancewa da shafin KuryaLoaded, gidan labaran duniya domin samun labaran mu kowace rana kuci gaba da bibiyar mu mungode.

2 comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *