Ni Shahararren Dan Tsibbu Ne Kafin Na Shiga Izalah – Sheikh Bello Yabo Sokoto

Posted by

Ni Shahararren Dan Tsibbu Ne Kafin Na Shiga Izalah – Sheikh Bello Yabo Sokoto

Kamar yadda mukayi karo da wani bidiyo inda babban malami Bello Yabo ya bada wani labari wanda ya shafi rayuwarsa wanda ya kira abun da tsoron labari amma karatu ya biyo ta wajen yasa ya bada wannan labari.

Kafin mu shiga cikin wannan jawabi da zamu gabatar muku da bidiyonsa a kasa yana dakyau ku san cewa amihad.com ta tattara wannan bayanai badan cin mutunci ko batawa wani suna ba.

Na daga cikin dalilan dayasa muka kawo wannan rahoto shine muhimmancin tuba ga Allah idan an aikata wani lafi ko kuskure wanda ya sabawa dokar Allah. Hakika ubangiji ya kira kansa da shi mai yafiya ne ga ko wane laifi da akayi masa in har anbi sharudan tuba.

Shiyasa muka kawo muku wannan labari domin tuni ga yan uwa musulmai akan yawan istigfari ga ubangijin halitta musammam a al’amuran rayuwar yau data kasance a na yawan aikata laifuffuka iri iri wanda suka sabawa wa dokar ubangiji.

Kazalika amihad.com ta kawo wannan labari da malam Bello Yabo ya bayar cikin bidiyon karatun daya gabatar a baya. Kuma sanin kowa ne malam ya bada wannan labari a matsayin laifi da yayi a baya kuma ya tuba a yanzu domin babu abinda yake cikin harkar tsibbu illa karya da yaudara kuma dukkaninsu manyan laifuka ne wajen mahalicci.

A cikin bidiyon da amihad.com zata kawo muku a kasa zakuji yadda mallam Bello Yabo yake cewa:

“Kafin mu shiga izalah, is an old story ai kasan munyi tsibbu ko, munyi tsibbu hmm!, Allah ya gafarta mana”Inji malam bello yabo

Malamin yace ba abinda ke cikin harkar tsibbu illa karya da yaudara kuma duk wani irin wannan harka ba’a rabashi da wadannan abubuwa.

Ya kuma bada labarin yadda aka kawo masa wani dan shaye shaye yayi masa magani inda ya kulleshi a daki ba abinda yayi masa amma saboda ya hanashi kayan shaye shaye hakan yasa yaron ya dawo hayyacinsa.

Bayan ya kammala wanan aiki ake tayi masa godiya bisa ceto rayuwar wannan yaro wanda a gaskiya kuma ba abinda yayi masa, koda kuwa addu’a baiyi masa ba.

Gadai bidiyon nan a kasa don ji ta bakin malam domin tabbatarwa da kanku.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *