Yadda Allah Ya Tona Asirin Wani Boka Me Lalata Da Matan Aure Dumu Dumu

Posted by

A rahoto da samu ya shaida mana cewa ’Yan sanda a jihar Bauchi sun kama wani boka da ake zargi da yi wa wata matar aure ciki a lokacin da ta kai ’yarta neman magani a wajensa.

Kamar yadda Aminiya ta rawaito kakakin rundunar a jihar, SP Ahmed Mohammed Wakil, ya ce wanda ake zargin mai kimanin shekara 32 na karamar hukumar Tafawa Balewa, ya yi amfani da kayan maye ne wajen gusar da hankalinta kafin ya yi mata fyaden.

Wakil ya kuma ce sun kama wani malamin makaranta mai kimanin shekara 25 da ake zargi da yi wa dalibarsa mai shekara bakwai fyade a karamar hukumar Alkaleri da ke jihar.

Ya ce, “Bayanan da ’yan sanda suka tattara sun nuna cewa wanda ake zargin, mazaunin unguwar Ajiya a garin na Alkaleri, malami ne a wata makaranta mai zaman kanta a garin.

“Jamia’nmu sun kuma kama wani mai sayar da askirin a garin Bauchi, saboda zargin yin luwadi ga wani yaro mai shekara 12 a bayan wani banki a Alkaleri.

Binciken farko-farko ya nuna wanda ake zargin ya sayi ruwan leda ne daga hannun yaron, sannan ya yaudare shi zuwa cikin wani shago ya yi lalatar da shi a ciki,” inji Kakakin ’yan sandan. (NAN)

kada kumanta kudinga muna share na post inmu zuwa ga abokaninku domin bamu qwarin guiwar kawomaku ingantattin sahihun labaran duniya a cikin harshen hausa dana turanci mungode da ziyartar shafin KuryaLoaded.ng dakunkayi

Idan kuna da tambaya ko wani labari da kuke son sanar da mu, ko tallata hajar ku kuna iya aika mana da sako a shafinmu na Facebook, ko tura sako a number admins dinmu +23408141702912

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *