EDUCATION

Shin Kokunsan Muhimman Sirruka 7 Na Saka Jigida Da Kuma Amfaninsu

Barka da Wannan Lokacin barkankuda ziyartar shafinmun Na KuryaLoaded Acikin Wannan rubutun Namu Mun Kawomaku Wani

Bincike Ko Rubutune Da Wani Shafin Yanargizo Na Amihad.com Yayi Akan Jigida Nasan Wasunku Zasu iyacewa basusan Minene Jigidaba

to Jigida dai itace Wannan Sarka Da Mata Ke Sakawa A Qugunsu  Acikin jigida Din Sun Kasu Kala Kala  Domin Kuwa har Ta Tsafi Ana Samu Aciki

kada na cikaku da surutu Ga Rubutun da Shafin Na Amihad.com yayi akan Jigidar anan Kasa Bayan kun karanta kumana Comments na Ra’yoyinku akai Mungode

Sirruka da amfanin jigida ga mata guda 7

1. A wasu yankunan ana hada jigida mata su saka domin samun kariya daga iska ko mutanen boye, wato aljanu.

2. Wani jigidan akan haɗa da surkulle ne domin wai ya kare mace daga kamuwa da cututtuka musamman kananan yara.
3. Wasu jigidan akan haɗa su mace ta saka a kwankwaso domin samun saukin naƙuda a lokaci haihuwa.

4. Akwai yakinin cewa saka Jigida na taimakawa wajen rage kiba musamman ga mata masu tumbi ko katon ciki.

5. Jigida na taimakawa wa mace wajen ƙara girman kugu wato Hips a Turance, dakuma samun farin jini cikin mutane

6. Jigida na ɗaya daga cikin abubuwan dake jawo sha’awa da ra’ayin namiji zuwa ga mace.

7. Mafi rinjaye daga cikin maza suna son gani mace sanye da jigida domin ta zama abin jawo hankalinsu.

Sai dai kuma duk da wadannan kyawawan dalilan wasu mutane da dama basu son jigida saboda a ra’ayinsu jigida sarka ne da ake amfani da shi domin wani tsafi.

Wata mata da ta shahara a hada jigida Felicia Musa ta ce tana matukar sha’awar jigida musamman idan mace ta saka shi yana kara idan tana tafiya.

Ta ce jigida iri-iri ne akwai wanda wasu matan ke sakawa na farin jini ko na samun kariya amma yi hakan ba shine ke mai da mutum matsafi ba.

Felicia ta ce saka jigida ra’ayi ne idan kana so ka saka idan ba ka so ba za ka saka ba amma rashin son shi din ba shine zai ba mutum daman cusa wa mutane ra’ayin kin shi ko rashin son shi ba.

 

Mr Kurya

The Name is Kurya An Full Time Blogger | Entrepreneur | Online Promoter| Web Designer | Web/App Developer | Content Writer | Your Number 1 B*D A** Blogger 😏 Follow Us Social Media Below

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Sorry You need to turn off your adblocker to browse on this blog please