Za A Kara Yanke Wani Sashe Na Kafar Fatima Sakamakon Rashin Yi Mata Aiki Mai Kyau A Farko
…karye ne Ali Nuhu bai ba ta tallafin naira milyan biyu ba, cewar ‘yan uwanta
Sakamakon rashin samun kyakkyawar kulawa ta hanyar yin aiki yadda ya kamata ya sa an garzayo da Fatima zuwa wani Asibiti dake Abuja daga Sokoto domin sake yanke wani sashe na kafarta.
Fatima wadda yanzu haka an shigo da ita Abuja, za a kara yanka wani sashen kafar na ta ne zuwa saman gwaiwar ta, kamar yadda rahotanni suka nuna, kasancewar aikin da aka yi mata a farko ba haka ya kamata ya kasance ba, wanda idan ba a yanke din ba zai iya jawo mata damuwa.
Idan ba a manta ba dai, Fatima ta gamu da tsautsayin yanke mata kafa ne sakamakon taka da wani dan makarantar su ya yi a yayin bikin kammala jarabawa a Sokoto.
Tun a farko dai Fatima Sulaiman ta soma jinya ne a asibitin UDUTH dake jihar Sokoto, kafin daga bisani aka garzayo da ita zuwa Abuja.
A gefe daya kuma yayan Fatima ya tabbatarwa da RARIYA cewa batun jita-jitar da ake yadawa cewa fitaccen jarumin finafinan Hausa, Ali Nuhu ya bada gudummawar naira milyan biyu domin jinyar kanwar tasa, ba gaskiya bane, labari ne mara makama bare tushe. Don haka ne ya yi kira da jama’a da su yi watsi da wannan jita-jitar.