Ina Masuneman Auren Bazawara Tsohuwar Matar Ado Gwanja Maimuna Tana Neman Mijin Aure Na Har Abada Duba Kuga Dalilin – KuryaLoded Blog

Posted by

Kamar yadda kuka sani cewa jarumin masana’antar kannywood kuma mawaki wanda, kukafi sani da Ado Isah Gwanja.

Yayi aure a shekarar dubu biyu dasha bakwai (2017) inda ya auri matar sa wato maimuna a garin jihar kano dake nigeria.

Mawaki ya angwace da budurwar ne, bayan wata yar gajeriyar Soyayya data kullu a tsakanin su cikin kankanin lokaci kafin yayi wuff da ita a gidan sa.

Maimuna matar Ado gwanja ta haifu dashi inda ta haifa masa jaririya santaleliya kafin daga baya wani dan sabani ya faru tsakanin su, har takai ga sun rabu da maimuna.

Bayan wasu lokuta masu tsawo mutane da dama suna tunanin ko mawakin ado gwanja ya mayar da matar tasa ne, maimuna dakin ta ashe ba haka bane.

Sai yau cikin wasu photuna da tsohuwar matar Ado Gwanja din ta saki a shafukan sada zumunta na Facebook, inda ta bayyana cewa tana neman mijin aure.

Yayin data bayyana cewa” ni Tsohuwar Matar Mawaki Ado Gwanja Wato Maimuna ina Neman mijin aure daidai dani wanda yake ga zai iya aure na kofa a bude take.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *