Innalillahi Hukumar Hisba Ta Kama Wani Dan Karamin Yaro Saboda Yazo Kano Ganin Ado Gwanja Tun Daga Jahar Adamawa

Posted by

Hukumar Hisba ta kama wani karamin yaro da yazo tun daga jihar Adamawa gurin ado gwanja.

Wani karamin yaro dai ya taso tun daga jihar Adamawa har kano inda yace yazo gurin ado gwanja yace shi cikakken masoyin sani yanajin wakokin sa da kuma fina finan shi tunba yanzu.

DUBA WANNAN: Fati Muhammad Ta Jawo Cece Kuce A Kafar Sadarwa Tare Maganganu Kan Talata Atiku Abubakar

Yazo domin haduwa da ado gwanjan kuma sun hadu inda akaga bidiyon haduwar tasu yana yawo hakan yasa hukumar hisba bankado inda yaron yake domin kamasi kuma su mayar da shi gurin iyayenshi a jihar adamawa.

Yanzu dai yayin faruwar haka ake inda akwanakin baya wani yaro yazo tun daga Niger gurun mawaki Ali jita domin nuna soyayya a gareshe.

Hukumar hisba dai ta kama yaron inda suka tambayi daga inda ya fito yace shi ɗan jihar Adamawa ne kuma yazo ne gurin ado gwanja domin ya nuna masa irin soyayyar da yake masa.

Hukumar ta hisba ta mayar da wannan yaron izuwa mahaifarsa dake jihar Adamawa.

Sai dai anji ta bakin ado gwanja inda yace shifa yana maraba da duk wani masoyansa daga ko ina suke a fadin duniya yayin ziyarar da yaron yazo dai ado gwanja ya bawa yaron kyautar kudi da kayan sawa.

3 comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *