Inason Nazama Hamshakiya Nafi Dangote Suna da Kudi Inji Tsohuwar Jarumar Kannywood

Posted by

Barkanku Da Zuwa Shafin KuryaLoded kamaryanda shafin namu yake kawomaku labarai akowane lokaci

yauma munzomaku da wata fira da tashar BBCHausa Tayi Da Tsohuwar Jarumar Kannywood Mainuna Wata Yarinya

Inda acikin Firar Tasu Ta shaidawa ‘Yan Jarida Cewa Ita

So Nake Na Zama Hamshakiyyar Mai Kudin Da Sunana Zai Danne Na Dangote Cewar Maimuna Muhammad

Gadai Yanda Cikakken Rahoton Yake Damuka Samo Maku

Ta ce za ta so duniya ta santa a wannan fagge na kasuwanci ta yadda zai kai sunanta ya danne na mai kudin Afrika kuma shahararren dan kasuwa, Alhaji Aliko Dangote.

Maimuna wata yarinya ta bayyana hakan ne a yayin wata hira da tayi da sashin Hausa na BBC a shirin ‘Daga bakin mai ita’. An tambaye ta menene babban burinta a rayuwa nan gaba inda ta ce

“Ka san shi dan adam yana da buri a rayuwa. Burina shine a duniyarmu ta yanzu da muke cikinta Ubangiji Allah yasa mu gama da duniya lafiya, shine burin mutum na farko. Sannan kuma burin mutum ba zai wuce yayi aure ya samu zuri’a dayyiba ba a rayuwa, toh wannan ma ina da buri.

Amman ni burina shine ina so na zama irin attajiran macen nan yar kasuwa. Wanda irin ace zan zo ma in danne Dangote a suna, sai ace Hajiya Maimuna wata yarinya. Ka ga kowa yana da burinsa amma ni ina so in zama attajirar yar kasuwa wanda duk duniya za ta san da ita.”

Wannan magana itace babbar burin wannan jarumar zaku iya samu cikakken bidiyan tattaunawar da akayi da ita a gidan talabijin din bbc hausa a shafinsu na instagram

Masu sauraranmu a koda yaushe bayan kun karanta wannan labarin zamu so karben ra’ayoyinku a sahen mu na tsoka

Kunji yanda firar ta kasance Ducigaba da ziyartar Mu Domin Samun Shahararrun Labarai Na duniya Acikin Harshen Hausa mungode

3 comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *