Abin da ya sa na kai wasu matasa kotu aka kulle su saboda ‘ya ta Iman – Mansurah Isah

Posted by


Shafin Filmmagzine Sun ruwaito WATA kotun majistare da ke Kano ta tura wasu matasa biyu gidan yari sakamakon ƙarar da tsohuwar jarumar Kannywood Mansurah Isah ta kai su.

Za a tsare su zuwa ranar Litinin kafin a dawo da su domin ci gaba da zaman shari’ar.

A bayanin da ta yi wa mujallar Fim, Mansurah ta ce ta yi ƙarar matasan ne bisa zargin su na amfani da sunan babbar ‘yar ta, Khadijatul Iman Sani Danja, su na aikata assha a shafukan su na soshiyal midiya.

Tun da fari sai da tsohuwar jarumar ta kai ƙorafi ga ofishin Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da ke Kano inda ta ce wasu na amfani da sunan ‘yar ta a Facebook, Instagram da TikTok su na yaɗa labarai da hotunan da ba su dace ba, duk da nufin Iman ɗin ce ta ke da waɗannan shafuka, alhalin ita sam ba ta hawa intanet da sunan ta, kuma babu wani shafi da ta ke yin amfani da shi na ƙashin kan ta.

Jami’an tsaron sun yi bincike har su ka kamo matasan guda biyu waɗanda ake zargi da laifin.

A jiya Juma’a aka gurfanar da su a gaban kotu domin ta ɗauki matakin da ya dace a kan su.

A zaman shari’ar dai na jiya, kotun ta tura matasan zaman riman na kwana uku.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa ana ci gaba da bincike domin a kamo ƙarin wani mutum ɗaya wanda ake zargin.

Ba mu samu jin ta bakin waɗanda ake zargin ba, amma bayan fitowa daga kotun mun tattauna da Mansurah, inda ta yi bayani kamar haka: “Abin da ya faru, duba da magunganun da ake yi a soshiyal midiya waɗanda ba mu mu ke yi ba, wanda za ka ga sharri ne ake yaɗawa, to mu iyaye mu kan jure da irin wannan sharrin da ake yi mana a YouTube da Facebook. Kuma ya zama su mutane ba su san abin da ya ke faruwa ba, daga an gani kawai sun ɗauka gaske ne su sun yarda da maganar.

“To wannan ya sa akwai wasu ɓatagari da su ka buɗe Facebook, TikTok, Instagram da sunan Khadijatul Iman Sani Danja, don haka duk idan ka shiga shafukan za ka ga duk da sunan Khadijatul Iman Sani Danja su ke amfani.

Kuma yaran nan duk mun bi su mun roƙe su mun ce don Allah su daina don ‘yar mu ba ta soshiyal midiya, kuma ba ma son su riƙa ɓata mata suna da hotunan ta, domin idan ka duba za ka ga sunan ta da yawa, kuma ba ta ma taɓa yin Facebook ba a rayuwar ta, amma za ka ga sunan ta da yawa wanda wasu yara matasa, maza, ƙanana, ƙazamai, wallahi su ne su ke buɗe Facebook ɗin.

“Kuma da mu ka bi su mu na ta roƙon su, su na tunanin sun fi ƙarfin a kama su. To wannan ya sa mun shiga damuwa mu iyaye, don haka mu ka je mu ka kai ƙara ga Hukumar Tsaro ta Farin Kaya.

“Kuma sun ɗauki lokaci su na bincike, don haka a yanzu sun gano mutane uku, sun kama mutum biyu, saura ɗaya, wanda a yanzu aka gabatar da su a kotu. Shi ma mu na sa ran zuwa gobe ko jibi za a kamo shi.

“A yanzu idan ka je Facebook za ka ga shafuka da suna na sun fi guda goma, kuma duk ba ni ba ce. Shafin da na ke da shi guda ɗaya, shi ne duk wani abu da na ɗora a Instagram ya ke hawa. Amma sai ka ga maganganu masu yawa, da wanda ka sani da wanda ba ka sani ba, amma dai mutane su na ganin kai ne ka yi shi, saboda hoton ka ne.

“Yanzu sau da dama idan na je wani waje sai a yi ta yi mani magana ana cewa na daina yawan surutu a soshiyal midiya, ni kuma ba magana na ke yi ba.

“Amma wai su su na yi ne don su samu mabiya a shafin kuma mu su na ɓata mana suna; kullum ana cewa na cika magana, ni kuma ba ni na faɗa ba.

“Yanzu ko a shekaranjiya ina cikin jirgi, wani ya tare ni ya na cewa surutun da na ke yi ya yi yawa a Facebook, ‘Ya kamata ki daina’. Wallahi sai da na ji kamar na yi kuka saboda na kasa gamsar da shi cewa ba ni ba ce don hotunan da ya ke gani nawa ne.

“To haka waɗannan shafuka da aka buɗe da sunan Khadijatul Iman Sani Danja su na saka hotunan tsaraici, su na haɗa hotunan ta da maza su na maganar banza ta batsa.

“To, irin wannan abubuwan ya na ɓata mana rai a matsayin mu na iyaye.

“Kuma mu na tafiya a kan hanya za ga an tare mu ana cewa ya za a yi mu bar ‘yar mu ta na Facebook? Kuma mun fito mun faɗa wa duniya ba ta yi, mutane ba su yarda ba. Sai mu ka ce tunda haka ne bari mu ɗauki mataki, don haka mu ka zo kotu don ta bi mata haƙƙin ta, saboda ta kai ko a makarantar su duk abin da su ka gani a Facebook sai su riƙa tambayar ta, ‘Ai jiya mun ga kin sa abu kaza a Facebook’.

Hatta malamin ta na Islamiyya sai da ya zo ya na yi mata faɗa a kan haka, ta yi ta rantsuwar cewa ba ita ba ce.

To ka ga wannan ya fara taɓa lafiyar ta, ya fara taɓa rayuwar ta, don haka dole ne mu iyaye mu taimaka wa ‘yar mu don samar mata da haƙƙin ta.

“Don haka duk waɗanda su ke buɗe Facebook da sunan Khadijatul Iman Sani Danja, to wallahi su sani zan ɗauki dukkan mataki na shari’a a kan su.”

Mansurah ta yi kira ga iyaye da su riƙa sanya ido a kan rayuwar ‘ya’yan su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *