KANNYWOOD

TIRKASHI Dalilin cire Ummi Alaqa ba zai fadu ba, zai iya taba mutuncinta, Jarumi Ali Nuhu

Dangane da shiri mai dogon zango na Alaqa wanda ya dauki hankalin jama’a da dama a makon nan bayan ganin an sauya jaruma wacce tauraronta ya fara haskawa, Habiba Y Aliyu wacce aka fi sani Ummi Alaqa ya bata wa masu kallo rai, Ali Nuhu ya magantu.

 

Mutane sun dinga surutai akan sauya jarumar inda wasu suke ganin saboda Maryam Yahaya ta fi ta fada ne a kamfanin yayin da wasu ke ganin kamar bakin ciki ake yi wa jarumar shiyasa aka cire ta aka mayar da Maryam.

Mutane da dama sun dinga surutai kowa yana tofa albarkacin bakinsa. Bayan ganin hakan ne yasa Tashar Tsakar Gida ta yi tattaki don samun mai shirya shirin kuma mai bayar da umarnin shirin, Ali Nuhu don jin albarkacin bakinsa.

Jarumi Ali Nuhu ya amsa tambayoyin da aka yi masa dangane da cire jarumar. Ya bayyana cewa yana da kwakkwaran dalilinsa na cire jarumar wanda hakan ne zai fi zama masa alkhairi, da jarumar da ma kamfanin gaba daya.

Ali Nuhu ya ce bayyana dalilin zai iya taba mutuncinta

Ali Nuhu ya bayar da hakuri inda ya ce ba zai iya fadin dalilin ba. Amma hakan shi ne alkhairi ga kamfanin da ita kanta jarumar.

Ya ci gaba da cewa cire jarumi ko sauya sa ba al’adar kamfanin FKD Productions bane amma tunda aka ga haka akwai kwakkwaran dalilin da yasa ba za a ji daga bakinsa ba.

Tashar Tsakar Gida ta so jin ko dai rashin kunya ta yi masa ko kuma wani babban jarumi amma Ali Nuhu ya ce sam ba haka bane.

Daga karshe Ali Nuhu ya ce abinda ya faru da ita abu ne da zai taba mutuncinta wanda yana da diya kuma ba zai so hakan ya faru da ita ba, shiyasa ya yi gaggawar cire ta.

Ya ci gaba da cewa yana fatan ta ji shawararsu ta yi aure ko kuma ta dan dakata da shirin na wani lokaci kafin aga abinda hali zai yi.

Muna fatan hakan ya zama mafi alkhairi, Ameen.

Mr Kurya

The Name is Kurya An Full Time Blogger | Entrepreneur | Online Promoter| Web Designer | Web/App Developer | Content Writer | Your Number 1 B*D A** Blogger 😏 Follow Us Social Media Below

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Sorry You need to turn off your adblocker to browse on this blog please